Labarai

Bazamu yarda da wannan abin kunya ba na dakatar da shirin N-power na wucin gadi ba – inji shugabanin matasan N-power

Biyo bayan wa’adin mako guda da muka baiwa gwamnati tarayyar Nijeriya jim kadan mun samu labari daga wasu kafafofin watsa labarai na kasa cewar Minista Dr Betta Edu ta ayyana kudirin gwamnati tarayya na dakatar da shirin N-Power na wucin gadi sakamakon binciken da kwamiti suka gudanar na cewar an samu almundahana da kudaden da ake fitarwa na N-Power ta bangaren manajoji da shashin nasims da ma tsohuwar Minista Sadiya Umar Farouq.

Wannan bincike ya sa aka dakatar na zuwa wani lokaci kafin daga bisani a biya wadanda suke bin bashin gwamnati tarayyar Nigeria allowance na watanni (9) wasu tunda aka fara ko gudanar da Npower program na Rukunin C ba’a taba biyansu sisin Kobo ba.

Bazamu yarda da wannan abin kunya ba na dakatar da shirin N-power na wucin gadi ba - inji shugabanin matasan N-power
Bazamu yarda da wannan abin kunya ba na dakatar da shirin N-power na wucin gadi ba – inji shugabanin matasan N-power

Don haka a iya sanina ba’a dakatar da mutum a aiki har sai an biya shi hakkonkin shi da yake bi bangaren ma’akatun gwamnati ne ko Kuma hukumomin masu zaman kansu na kasa wannan dokace don haka lokaci yayi da zamu nuna munsan hakkin mu Kuma Mun samu ilimi da gogewa a dukkan bangarori

Saboda Haka Minister da tagaya mana sakon su mun ji mun gani muma muna Fatan zasu saurare namu sakon Zangar Zangar lumana a duk fadin kasar ranar 18 Oct 2023

Ni comrd Muhammad Habibu abubakar gmb shugaban masu cin gajiyar shirin Npower na kasa na samu daman umartar dukkan ciyamominmu na Npower na gundumomi akan su fito da mutanen su na jihohin don gudanar da zangar-zangar Lumana a jihohin 36 da FCT Abuja. Sannan na umarce su da tabbatarwa a duk jihohin a Ranar zanga-zangar an ziyarce muhimman wurare kamar NUJ office na kowacce jiha da House of assembly dama focal person office na Npower da government house da-dai sauran Muhimman gura-gurare

Daga karshe muna Kira ga dukkan kafafen watsa labarai na kasa Kuma Yan kishin kasa ko Kuma Yan gwagwarmayar na social media dama wasu manya a kasar masu fada aji Kuna iya! bada taku gudamawar domin al’ummar kasar masu amfana da Shirin na Npower Kuma Kuna iya
Tuntubar mu a numbobin wayar Kamar Haka .

1– NATIONAL CHAIRMAN
COMR’D MUHAMMAD HABIBU ABUBAKAR (GMB) 07065315951

2-VICE CHAIRMAN
COMR’D SANI IDRIS
08109970324

3–NATIONAL SECRETARY
BASHIR LADAN
08033609598







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button