An soma shiga da kayayyakin agaji Gaza daga kasar Masar


Rukinin motocin farko dauke da kayayyakin agaji daga Masar sun soma shiga Gaza da aka yi wa kawanya ta iyakar Rafah, kamar yadda wani jami’in tsaro da kuma wani ma’aikacin kungiyar agaji ta Red Cross ta Masar suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Sama da manyan motoci 200 dauke da kusan tan 3,000 na kayayyakin agaji ne aka jibge a Rafah din tsawon kwanaki kafin suka soma shiga cikin Gaza.


Mutane da dama a Gaza sun koma cin abinci sau daya a rana ba tare da samun ruwan sha ba, inda suke tsananin jira domin kai musu kayan agaji.majiyarmu ra samu labarin daga jaridar TRTAFRIKA Hausa.
Haka kuma ma’aikatan asibiti sun damu matuka sakamakon karancin kayayyakin kiwon lafiya da kuma man fetur da za a saka wa janareto domin samun wutar lantarki a asibitocin,
Wani labari na daban: Adewale Adeniyi ya zama shugaban kwastam
Shugaba Bola Tinubu ya amince da tabbatar da Adewale Adeniyi a matsayin Kwanturola-Janar na hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS).
Wannan dai na zuwa ne kusan watanni hudu bayan da shugaban kasar ya nada Adeniyi a matsayin mukaddashin shugaban hukumar bayan sallamar Kanar Hameed Ali (rtd).