Labarai

Abinda yasa anka kama Fiddausi yar Tiktok

Yanzu nan munka wallafa muku labarin yadda jami’an tsaro sunkayi awon gaba da Fiddausi da yar Tiktok da ke kano wanda wasu basu san asalin dalilin faruwar hakan ba shine yanzu munka samu abinda ya sanya jami’an kama Fiddausi yar tiktok kamar yadda fitaccen marubucin nan Datti Assalafiy na wallafa a shafin na facebook.

“Jama’a zaku tuna wannan yarinyar da tace a madadin a kwace wa Gwamnan Kano Abba Kujeransa gara a bata b0m taje ta káshe mutanen da suke da hannu a ciki

Ta kama sunayen mutane kamar haka:
(1) Alkaliyar da ta jagoranci yanke hukuncin
(2) Tsohon Gwamnan Kano Ganduje
(3) Mawaki Rarara
(4) Nasir Yusuf Gawuna
(5) Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima

Banda munanan zaginsu da tayi gaba dayansu sai da tace zata rataya b0mb ta tashesu su tárwatse gaba daya

A halin da ake ciki yanzu jami’an tsaron sirri sun je gidansu yarinyar da tsakar dare suka kamata suka tafi da ita inda ba’a sani ba, Mahaifiyarta tana ta kuka take bada sanarwan kama yarinyar

Abin takaici yarinyar ‘yar uwan mu ce talaka, ba wani karfi suke da shi ba a gidansu, gashi nan yanzu ta jawowa kanta, kuma babu wani mutum duk girman matsayinsa da zai tsaya mata saboda furucin kunár bakjn wake da b0mb da tace zatayi

Ina ganin da a zagin kadai ta tsaya tayi to da ba za’a kamata ba, amma alwashi tayi cewa sai ta rataya b0mb ta tarwâtsasu

Ya kamata jama’a su gane wani abu a siyasa, idan kai tarbiyyan ashar kake dashi babu wanda zai hanaka kayi zagi ko suka a siyasa, amma ka kiyaye yiwa wani barazana da rayuwarsa idan kana son ka kwana gidanku lafiya kenan

Abinda wannan yarinyar tayi yana da nasaba da yarinta da rashin tarbiyya, na tausaya mata”

A yanzu haka dai jami’an tsaro sun haura cikin gidansu sunyi awon gaba da ita duba da irin ikirarin da wannan yarinya take na kalamai marar daɗin ji ga kadan daga cikin kalaman.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button