Labarai

Wani mutum ya wulakanta Alkur’ani a wajen Ofishin Jakadancin Turkiyya na New York

Jami’an tsaro sun yi gaggawar shawo kan lamarin, inda suka fitar da mutumin daga harabar ginin da karamin ofishin jakadancin Turkiyya da na Majalisar Dinkin Duniya suke.

Jaridar TRTAFRIKA Hausa na ruwaito Wani mutum da ba a bayyana sunansa ba ya jefar da Alkur’ani mai tsarki a kasa, ya tattaka shi a wajen ginin da karamin ofishin jakadancin Turkiyya ko Turkevi yake a birnin New York na Amurka.

Wani mutum ya wulakanta Alkur'ani a wajen Ofishin Jakadancin Turkiyya na New York
Wani mutum ya wulakanta Alkur’ani a wajen Ofishin Jakadancin Turkiyya na New York Hoto/Gettyimage

Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da misalin karfe biyu da arba’in da shida a agogon GMT, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyya ya rawaito.

Jami’an tsaron ofishin jakadancin Turkiyya sun yi gaggawar daukar mataki inda suka fitar da mutumin daga ginin, wanda ke dauke da Karamin Ofishin Jakadancin Turkiyya da wani ofishi na Majalisar Dinkin Duniya.

Alkur’anin da mutumin ya wulakanta wanda aka fassara da Turancin Ingilishi ne.

An shaida wa Jami’ai a ofishin rundunar ‘yan sandan New York (NYPD) da Jami’an Tsaron Ofishin Jakadanci (DSS) faruwar lamarin.

Wani bidiyo da aka watsa a soshiyal midiya ya nuna mutumin yana jifa da Alkur’ani a kasa sannan ya tattaka shi yayin da yake ihu yana cewa “Wannan Alkur’ani ne.”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button