Labarai
Wani Bawan Allah Ya Gwangwaje Matashin Da Ya Mayar Da Kuɗin Nan Da Adaidaita Sahu


In Baku manta ba shine wanda ya tsinci Naira Miliyan 15 kuma ya mayar wa maishi bayan yaji sanarwa a Arewa Radio 93.1.
Sakamakon wannan abin kirki da yayi, Alhaji Bashir Gentile ya kai yaron gidan wani Babban Mai Arziki anan Kano, inda ya bashi wannan sabon adaidata sahu don Wanda Yaron yake amfani da shi na haya ne. Kuma yayi ummarni a maidashi ya koma makaranta, ya dauki nauyin karatunsa har Sai ya gama.
Wani labari na daban Dan darman sokoto yayi masa kyauta.
Alh. Mustapha Garba, Dandarman Sokoto ya bashi kyautar naira dubu 100, da shaddoji domin ƙarfafa guiwarsa shi da mahaifinsa.