Labarai

Sheikh Abubakar Giro ya ya gyara tarbiyyar al’umma a ayyukansa – tsohon shugaban kasa Buhari

Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Sheikh Abubakar Giro Argungu sakamakon rasuwarsa bayan gajeriyar jinya ranar Laraba.

Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalai da mabiyansa,” in ji Buhari, yana mai addu’ar “Allah ya ji ƙan sa, ya saka shi cikin Jannatul-Firdaus”.

“Ya tsaya kan ɗabi’un Musulunci tare da nuna jajircewarsa a aikace wajen gyara tarbiyyar al’umma ta hanyar wa’azinsa da ayyukansa.”

A jiya Alhamis aka yi jana’izar malamin a masallacin Idi na garin Argungu da ke jihar Kebbi, inda dubban mabiyansa suka halarci binne shi.

Malam ya samu miliyoyin mutane da sunka halarci jana’izarsa wanda tabbas musulunci yayi babban rashi Allah yayi masa rahama yasa aljannah ce makomarsa amen.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button