Rahama sadau ta bayyana alakarta da Ali Nuhu


- Abubuwan da ke ciki
- Kin taba da na sanin yin wani abu
- Menene alakari da Ali Nuhu
- Rahama Sadau ta bayyana mutane ukku da ba za ta manta da su ba a kannywood
Shaharariyar jaruma masanantar kannywood Rahama sadau tayi fira da gidan jaridar TRTAFRIKA inda ankayi mata tambayoyi sosai akan abunda ya shafi rayuwarta.
Kin taba da na sanin yin wani abu?
Da zarar abu ya faru da ni nake daukarsa a matsayin darasi , saboda haka babu batun na yi da sani kawai dai nayi abin da ya jawo magana, sai na dauki darasi na ci gaba da rayuwarta shikenan.
Sai kuma a kula da gaba, abin da nake gaya wa kaina kenan..


Gaya mana mutum ukku da ba za ki manta da su ba a kannywood?
“Idan kace na fadama zan iya cewa Ali Nuhu, Ali Nuhu, Ali Nuhu amma bari a barshi matsayin daya Ali Nuhu, yaseen auwal akwai Ali Nuhu..
Menene alakari da Ali Nuhu?
“Rahama sadau : Ali nuhu uban gida ne, gwani ne kuma mai gidan kowa , kuma ya bani gudunmuwa sosai a rayuwata kusan in ce kashi Casain zuwa dari na rayuwata a kannywood da yadda na taso, da kula dani.
“Ya bani kariya a matsayin uban gida kuma na gode masa kuma a kowacce masana’anta idan ka shiga dole kana bukatar wanda zai dora a turba saboda haka ina ganin girmansa sosai.”
Ga bidiyo hirar nan.