Labarai

Bayani kan bashin $700m da Bankin Duniya ya bai wa Nijeriya don tallafa wa mata

Bankin Duniya ya ce ya bai wa Nijeriya bashin dala miliyan 700 domin tallafa wa shirin nan na mata mai suna ‘adolescent girls’ learning and empowerment’ wanda ke tallafa wa mata samun ilimi da kuma karfafa su.

Bankin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na intanet a ranar Juma’a.jaridar TRT Afrika na ruwaito.

Ya ce makasudin bayar da wannan kudin shi ne kara yawan jihohin da ake yin wannan shirin da kuma shigar da matan da ba su zuwa makaranta a ciki da masu nakasa.

Bayani kan bashin $700m da Bankin Duniya ya bai wa Nijeriya don tallafa wa mata
Bayani kan bashin $700m da Bankin Duniya ya bai wa Nijeriya don tallafa wa mata

“Bankin Duniya ya amince da karin dala miliyan 700 ga Nijeriya domin habaka shirin ‘Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment program’ wanda burinsa shi ne kara samar da dama ga karatun sakandare ga mata a jihohin da ake shirin.

“Karin kudin zai habaka shirin daga jihohi bakwai da ake yi a yanzu zuwa 11 da kuma kara yawan matan da suke amfana wadanda suka hada da wadanda ba su zuwa makaranta da masu aure da kuma masu nakasa,” in ji sanarwar.

A cikin shirin na AGILE wanda a halin yanzu ake yin sa a jihohin da suka hada da Borno da Ekiti da Kaduna da Kano da Katsina da Kebbi da Filato, adadin yaran da ke zuwa makaranta ya karu daga dubu 900 zuwa miliyan 1.6, in ji bankin.

Haka kuma a karkashin shirin, an gyara sama da dakunan karatu 5,000 sa’annan sama da mata 250,000 sun samu tallafi.

Bankin ya bayyana cewa Nijeriya na da sama da yara miliyan 12 zuwa 15 wadanda ba sa zuwa makaranta inda bankin ya ce akasarin yaran na Arewacin Nijeriya, yankin da adadin matan da ke kammala sakandare ke kasa da na kudancin kasar.

Bankin ya kuma bayyana cewa akwai karin rikice-rikice da tarzoma a kusa da makarantu da ya shafi sama da yara miliyan daya tun daga 2020 zuwa 2021, lamarin da yasa da dama daga cikinsu ba su koma makaranta ba.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button