

Ibrahim, wanda kuma shi ne baban ɗan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, yayin da yake jawabi ga ’yan jarida a Bauchi, kan shirye-shiryen bikin Mauludi na bana.
Ya kuma roki mutane, musamman malamai, da su kauce wa muzanta juna da sunan wa’azi.jaridar Aminiya na ruwaito.
Ya ce mutuntawa da fahimtar juna da kuma amfani da dadaddiyar al’adar zaman lafiya sun zama wajibi muddin ana son samun ci gaba.


Sheikh Ibrahim ya kuma bukaci ’yan Najeriya da su daina tsinewa shugabanninsu saboda matsin rayuwar da suke ciki a yanzu.
“Matsi da walwala duk daga Allah suke. Abin da ya kamata ’yan Najeriya su yi a wannan lokacin shi ne su koma ga Allah sannan su kyautata zaton abubuwa za su canza,” in ji malamin.