Labarai

Yar gidan talaka mai tallan Goro ta zama Minista a Najeriya

Hannatu Musa Musawa, da ta fito daga jihar Katsina ta fashe da kuka a yayin da ake kokarin tantance ta domin zama Minista a Gwamnatin Bola Tinubu, jiya Talata a majalisar dattawan Najeriya.

Hannatu ta bada labarin yadda mahaifinsu ya taso a matsayin talaka da ke tallar Goro, daga baya ya kokarta ya samu ilmin boko.Yar gidan talaka mai tallan Goro ta zama Minista a Najeriya

Ganin mahaifinta Alhaji Musa Musawa ya rasu ana saura watanni 4 za a zabi ‘yarsa domin ta zama Ministar Tarayya, shiyasa ta fashe da kuka da hawaye a majalisar.

Hannatu tace ta so ace mahaifinta yana da rai ya ga ‘yarsa ta zama minista, saboda sun taso ne a cikin tsananin talauci, kafun daga bisani Allah ya budawa mahaifin nata.

Akwai darussa da yawa da ya kamata duk wani Musulmi ya dauka a cikin labarin da ta bayar, ni kaina ta sosa mun zuciya.

Muna yiwa Lauya Hannatu Musa Musawa, fatan Alkhairi tare da Addu’ar Allah ya bata ikon sauke nauyin da aka daura mata, Allah yasa wannan mukamin nata ya amfani Addinin Musulunci da talakawan Najeriya baki daya, Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Rubutawa: Comr Abba Sani PantamiMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button