Yanzu -yanzu : yan bindiga sun saki bidiyon da sunka yiwa sojoji kisan gilla (bidiyo)


Wasu gungun barayi ‘yan ta’adda a kauyen Kundu dake kusa da garin Zungeru karamar hukumar Wushishi jihar Niger sun yiwa tawagar Sojojin Nigeria mummunan harin kwanton bauna. Fitaccen marubuci nan Datti Assalafiy ne ya fitar da Wannan rahoto.
A kalla zaratan mayakan Sojojin kundubala 23 har da wasu manyan ofisa na Soji sun amsa kiran Allah, wannan shine hari mafi muni da ya taba rundinar Sojin Nigeria a wannan shekara
Sannan akwai wani jirgin yakin sojojin saman Nigeria shima yayi hatsari a jihar Niger wanda har zuwa yanzu ba’a fitar da bayanai akan dalilin ruftowar jirgin ba
‘Yan ta’addan Boko Haram da ISWAP da Ansaru da masu garkuwa da mutane sun yi karfi sosai a jihar Niger
Ya kamata Shugaban Nigeria Tinubu ya nemi agajin Sojojin ECOWAS a turasu jihar Niger, Zamfara, Katsina da Sokoto Yaki, domin ‘yan ta’adda sun yi juyin mulki a wasu yankuna na Jihohin, kuma suna cigaba da salwantar da rayukan fararen hula har da Sojoji
Muna rokon Allah Ya karbi shahadar Sojojin da aka kashe a Niger.
Ga bidiyon nan.