Labarai

Amarya ta kashe Angonta ta hanyar caka masa wuka a Bauchi

Yanzu nan majiyarmu ta hausaloaded samu daga wani fitaccen marubuci a shafin sada zumunta facebook mai suna Datti Assalafiy inda ya wallafa rubutun kamar haka.

Yau a cikin garin Bauchi a wata unguwa da ake kira Dumi wata mata ta halak mijinta ta hanyar caka masa wukã suka uku a kirjinsaAmarya ta kashe Angonta ta hanyar caka masa wuka a Bauchi

Zuwa yanzu dai babu wanda yasan dalilin da yasa ta kâshe mijinta, zan je State CID Bauchi na bi diddigin dalilin da yasa wannan yarinya ta káshe mijinta na aureAmarya ta kashe Angonta ta hanyar caka masa wuka a Bauchi

Abin takaici, da wahala kaji miji ya kashé matarsa, yawanci sai dai a ji mata ta kashé mijinta

Maza ku dinga sanin irin matan da zaku aura ta hanyar nazari da karantar halayyarsu idan suna cikin bacin rai

Mafi kololuwar laifi a tsakanin ma’aurata shine miji yazo ya tarar da kwarto a kan matarsa, ko mata tazo ta tarar da mijinta akan kwartuwa, ba duka ba zagi, a rabu kawai rabuwa na har abada, Allah Zai yi sakayya

Zaman aure ba dole bane, shiyasa Allah Ya halasta rabuwa idan akwai cutuwa, cin amana, zargi ko zalunci a tsakanin ma’aurata

Allah Ya sauwakeMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button