Labarai

Zan daina TikTok amma ina rokon kwamandan Hisbah, Ibn Sina da ya aure ni — Hafsah Fagge

Shahararriyar yar TikTok ɗin nan, Hafsah Fagge, ta ci alwashin zubar da makamanta ta rungumi rayuwar tarbiyya da zaman lafiya.Zan daina TikTok amma ina rokon kwamandan Hisbah, Ibn Sina da ya aure ni — Hafsah Fagge

Sai dai kuma ta ce bayan ta daina saka bidiyo na rashin dacewa, tana rokon Babban Kwamandan hukumar Hisbah, Muhammad Harun Ibn Sina da ya aure ta.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa Hisbah ta baza komarta ta neman Hafsah ruwa a kallo biyo bayan faya-fayan bidiyo na shakiyanci da ta ke wallafa wa a kafar TikTok.

Sai dai kuma da ta ke shaida wa Freedom Radio Kano, Hafsah ta ce ta daina dauka da wallafa irin wadannan bidiyo, inda ta kara da cewa ta tuba ta dena.

Ta kuma ƙara da cewa ta yi hakan ne bisa rashin sanin illar hakan, inda ta media tafiyar hukumar Hisbah da kuma al’ummar Musulmi baki ɗaya.

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, Hafsah ta shaida wa Freedom Radio cewa idan ta daina rawar TikTok, tana rokon Ibn Sina da ya aure ta domin ta sake samun nutsuwa.

“Na yi alkawarin na daina TikTok. Na gano cewa bai dace ba. Ina rokon Hisbah da al’ummar Musulmi da su yafe min.

“Sannan kuma ina rokon shugaban Hisbah, Ibn Sina da ya aure ni domin mutumin kirki ne kuma yana kira ga abin Allah , ya na kuma yin da’awa da yaɗa tarbiyya,” in ji Hafsah.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button