Kannywood
Burina ‘ya’yana su gajeni a fim amma su ƙi – cewar Ali Nuhu
Fitaccen tauraron fina-finan Hausa na Kannywood Ali Nuhu ya ce inda don ta shi ne ya fi so ɗansa ya gaje shi a harkar fim.
To amma kuma a cewarsa ɗan nasa ya fi sha’awar harkar ƙwallon ƙafa, dalilin da ya sa kenan ya mara masa baya, domin ya cimma burinsa.
Ali Nuhu ya ce ”abin da zamani ya zo da shi yanzu shi ne, idan ka ga ɗanka ko ‘yarka na son wani abu, matuƙar bai saɓa wa addini ba to ka goyi bayansa, ka ba shi ƙwarin gwiwa wajen cimma burinsa.”
Ya ƙara da cewa kar ka tilasta wa yaro kan dole cewa sai ya yi wani abu.
Zaku iya sauraren wannan hirar da Bbchausa sunkayi da shi kai tsaye daga bakin sa.