Bidiyo : Gaskiyar Zancen baiwa Rarara Gida ko Mota – Daga bakin Babban chinedu
Babu Wanda Ya Baiwa Rarara Gida Ko Mota - inji babban chinedu
A kwanakin baya anyi ta yada wasu labarai cewa gwamna aminu masari ya baiwa rarara gida da mota sai wani kuma shahararen attajirin nan Dahiru mangal ya ba bashi sabuwar motal dal cikin leda inda duk wannan labari kanzon kure ge ne.
Wanda babban chine yasa yayi wani bidiyo yazo yana bayyani dalla dalla akan wannan abu da ya faru garesu wanda zamu dora muku bidiyon domin kuji da kunnenku.
Kuma Ni Ma Babu Wanda Ya Ba Ni Komai Akan Asarar Da Muka Yi, inji shi mawakin Baban Chinedu.
Baban Chnedu ya kuma ƙara da cewa “maganar baiwa Rarara gida da mota kamar yadda wasu ƙafofin sadarwa suka yaɗa duk ƙarya ne, kuma ni ma babu wanda ya ba ni koda kwano akan abinda ya faru da mu.
Baban Chinedu ya ci gaba da cews “Bana tunanin akwai ɗan siyasar da zai iya biyan Rarara asarar kuɗin da ya yi lokaci ɗaya, akwai su, amma yin hakan ne abu mai wahala, domin ya yi asara sosai, ko ni ma nan na yi asara ta haura milyan arba’in. Kuma duk inda aka kama kaya a wurin ƴan sanda a Kano babu inda babu kayana”.
Ga bidiyon nan ku saurara kuji.