Kannywood

Yan Nigeriya aje tsofaffin kudinsu idan Tinubu yaci zaɓe za’a cigaba da amgani da su – cewar Rarara

‘Yan Nijeriya Su Tanada Tsoffin Kudadensu Domin Idan Tinibu Ya Ci Zaɓe Za Su Cigaba Da Amfani Da Su – Mawaki Rarara

Majiyarmu ta samu wani rahoto da shafin Rariya a shafinsu na sada zumunta inda suke cewa mutane su boye kudinsu tsofaffi idan har tinubu yaci zabe acigaba da amfani da kamar yadda sunka ruwaito.Yan Nigeriya aje tsofaffin kudinsu idan Tinubu yaci zaɓe za'a cigaba da amgani da su - cewar Rarara

Fitaccen mawaƙin nan na siyasa Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa “wannan tsari na canjin kuɗi ana yi ne domin kawo tasgaro ga ɗan takarar nasa na jam’iyyar APC, mawaƙin ya nuna zarginsa ƙarara ga gwamnan babban banki, wato Emefiele, sannan kuma ya bayyana koda shugaba Buhari aka kitsa wannan al’amari to tabbas Buhari ya tafka kuskure.

Mawaƙin ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su ajiye kuɗinsu, domin idan Tinibu yaci zaɓe za su ci gaba da amfani da su, domin za su cire Gwamnan na CBN domin jama’a suci gaba da amfani da tsoho kuɗinsu, sannan a karshe ya bayyana ƙarin kwana goma amatsayin aikin banza.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button