Labarai

Yadda Matar Aure ta Mayar Da Mijinta Shalele ya motsa mutane sosai

Wani bidiyon yadda wata matar aure ke kula da mijintaya ɗauki hankulan mutane a yanar gizo.

A cikin bidiyon an nuna matar tana ba mijinta abinci a baki yayin da yake saurin shiryawa domin tafiya wurin aiki saboda ya makara. Jaridar dimokuraɗiya ta rahoto

Yadda Matar Aure ta Mayar Da Mijinta Shalele ya motsa mutane sosai
Yadda Matar Aure ta Mayar Da Mijinta Shalele ya motsa mutane sosai

Bidiyon mai ɗaukar hankali dai Sam’an Ali Muazu ya sanya shi a LinkedIn inda ya yaba da abinda matar tayi.

Ali yayi nuni da cewa kowane namiji yana buƙatar mace ta gari a rayuwar sa, ko da kuwa matar nan zata kasance ƙawa ce kawai.

A cewar sa, mace ta gari tana ƙara wa namiji daraja a rayuwar sa komin ƙanƙantar abinda take masa.

A cikin bidiyon, matar ta tsae ɗaure da zani tare da mijinta inda take ciyar da shi yana sanya kaya, tana yi tana ci daga abincin.

Bayan ta kammala ba shi abincin, sai ta ba miƙa masa gorar ruwa kafin ya tafi.

Mutane sun tofa albakacin bakin su

Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana:

Adam S. Adam ya rubuta:

Abin sha’awa. Dama ace nine… Don Allah ku taya ni addu’a na samu mace ta gari.

Okeowo Adeboye Opeyemi ya rubuta:

“Gwarzuwar matar shekara.”

Bright Richard ya rubuta:

“Wannan shine abinda abota ke kawowa a aure. Yin hakan abu ne mai kyau. Wannan ba maganar matsayi bane ko kuɗi.

Fatima Hussaini ta rubuta:

“Shine yake samar da farin ciki a gidan., kowace mace itama tana buƙatar miji na gari. Ba ku lura cewa baya da komai ba, saboda haka ba za mu iya gane farin cikin su ba har sai mutumin ya samu arziƙi.

Boniface Alimwene ya rubuta:

“Shin kwanannan aka ɗauki bidiyon nan? Na yi amanna cewa irin waɗannan mata ba a samun irin su a yanzu. Allah yayi miki albarka.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button