Kannywood
Yadda anka gudanar jana’izar Jarumi Kamal Aboki
Allahu Akbar Lokaci yayi babu tsayawa dole mutum ya karba kiran mahalicinsa a yau din nan an gudanar da jana’izar Shahararren dan wasan barkwaci Kamal aboki da jiya sunkayi hatsari a mota.
Kamal aboki matashin jarumi ne da yayi fice wajen wasan barkwanci da ake arewacin Nigeriya inda yayi suna sosai wanda yaron hayana da hikima da azanci da fara’a.


Mutane da yawa sun halaci jana’izar wannan matashin yaron da ankayi a yau inda duban mutane da abokan sana’arsa sunka hallara a wajen.
Muna yiwa wannan matashi kyawawan zato domin irin yadda yayi zama da mutane Allah ya jikansa yayi masa rahama amen, ga bidiyon yadda ankayi sallah har i zuwa gidansa na gaski nan kasa zaku iya kallo.