Labarai

Wasu Abubuwan Da Yakamata Kasansu Kamin Ka Soma Soyayya Da Bazawara Mai ‘Ya’ya

Kamar yadda kasani zaurawa kala, kala ne, sai dai ita bazawara mai yara tafi wahalar soyayya cikin jerin zaurawan da ake dasu. Don haka kamin ka soma soyayya da ita ya dace ka san wadannan abubuwan domin sune zasu taimaka maka a tafiyar da soyayyar ka.

1: ‘Ya’Yan Ta: Bazawara mai yara abu na farko dake gabanta wajen duk wani wanda zai sota shine makomar yaranta a wajen mai sonta.
Dole idan kana son ka sace zuciyar bazawara mai yara sai ka so ‘ya’yan ta soyayya kuma na gaskiya fiye da wanda kake mata.

Idan yaran suna tare da ita zaka iya daukan nauyinsu su dawo gabanka. Idan kuma suna tare da mahaifinsu ko ‘yan uwan mahaifinsu kana maraba dasu a duk lokacin da zasu kawo muku ziyara na kwana biyu.
Wadannan abubuwan sune bazawaranka zata soma neman amsarsu daga gareka. Muddin ta fahimci kana kyamar yaranta kamar yadda akasarin maza suke yi, zata hakura dakai duk irin son datake maka. Yakamata ka san wannan.

Wasu Abubuwan Da Yakamata Kasansu Kamin Ka Soma Soyayya Da Bazawara Mai 'Ya'ya
Wasu Abubuwan Da Yakamata Kasansu Kamin Ka Soma Soyayya Da Bazawara Mai ‘Ya’ya

2: Tsohon Mijinta: Ko kana so ko baka so sai mu’amala ya hadasu da tsohon mijinta. Kodai ta waya ko kuma gaba da gaba.

Idan kuma mijin nata marigayine dole zata yi mu’amala da na kusa dashi saboda abunda aka haifa. Kanada hakurin da zaka daurewa hakan.
Muddin bakada hakurin hakan kada ma ka tinkari auren bazawara mai yara domin ko tace maka babu abunda zai shiga tsakaninta da tsohon mijinta ko ‘yan uwansa kuma suna da yara zance ne kawai zata yi hulda a munafurce kenan.

Don haka ka sani muddin soyayya zakayi da bazawara mai yara to kayi hakurin ganinta da tsohon mijinta idan ya kama, ko jinsu ta waya, ko kuma ‘yan uwansa.
3: Mutuncinta: Bazawara mai yara tana son ganin wanda yazo nemanta da aure zai mutuntata ya kuma girmama halin daya sameta a ciki.

Wasu mazan sukan yiwa irin wadannan matan gori ko bakar magana bayan sun dauki dawainiyarsu daya yaransu.
Ka sani babu abunda zaka yiwa gori ko bakar magana bayan ka auri bazawara mai yara. Idan kasan kai irin mazan nan ne masu gori ko furtawa mata maganar daya fito a bakinsu, to ka hakura da auren bazawara mai yara ba laying ka bane.

4: Rashin Sakin Jiki: Dole ne kayi hakuri da yadda zaka soma soyayya da duk wata bazawara musamman wanda take ganin mijin daya sake ta ya ci amanar ta idan sakinta akayi. Bare kuma wacce aka rabu da yara a tsakani.
Idan kuma mutuwa yayi nan ma sai kayi jimriyar baka labarin marigayi irin soyayyar dayake mata koda kuwa dukanta yake yi.
Irin wadannan matan basa saurin yarda da maza Saboda tunanin mazan da suka auresu suna ‘yan mata ba da akaci soyayya gashi yanzu sun sakesu. Wannan yasa sai ka dau lokaci kana lallaminta kamin nan ta tabbatar da gaske kake kuma tana sonka sannan ta amince maka.
Kada kayi tunanin cewa irin wadannan zaurawan zaka samu kansu cikin sauki. Domin wasu ma ganin suke su da aure kuma zancen ya kare saboda kuncin da mazansu na baya suka jefasu.
Wannan yasa idan har zakayi soyayya da bazawara mai yara. To kayi hakurin shawo kanta.

5: Kushen Na Kusa Dakai: Komai tsufanka koda kayi jika da bazwaran da take da yara. Koda yaran dake gidanka sun ninka nata, da ka tashi neman aurenta sai ka samu na kusa dakai da zasu kushe ta.
Don haka ka shiryawa wannan kushe muddin zaka yi soyayya da bazawaran da take da yara.

Wadannan sune abubuwan la’akari wajen neman bazawara mai yara. Da fatan zaka shiryawa duk wani kalubalen da zai tinkaroka wajen neman aurenta.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button