Labarai

Soyayya Daɗi: Yadda Wani Matashi Ya Sanya Aka Yanka Hannunsa Domin Rubuta Sunan Masoyiyarsa

Wasu abubuwan da masoya ke yi a wasu lokutan na domin nuna irin son da suke wa abun ƙaunar na su na matuƙar ɗaure wa mutane kai. Shafin dimokuraɗiya na ruwaito.

Soyayya Daɗi: Yadda Wani Matashi Ya Sanya Aka Yanka Hannunsa Domin Rubuta Sunan Masoyiyarsa
Soyayya Daɗi: Yadda Wani Matashi Ya Sanya Aka Yanka Hannunsa Domin Rubuta Sunan Masoyiyarsa

Hakan shine abinda ya faru da wani matashi wanda ya sanya aka yanka fatar jikin sa aka rubuta sunan masoyiyar sa.

A wani bidiyo da shafin Linda Ikeji ya sanya, ya nuna matashin wanda yake sana’ar siyar da kayan ɗauke da sunan masoyiyar ta sa rubuce a hannun sa.

A cikin bidiyon an nuna matashin tsaye a cikin wurin sana’ar sa ga kuma kayan miyar sa nan a wurin.

Daga nan sai kyamarar ɗaukar bidiyon ta zuƙo domin nuna yadda aka rubuta sunan Zainab raɗau rubuce a hannun sa.

Yankar da akayi masa wajen rubutun dai sabuwa ce domin a na iya ganin jini a jikinta.

Sannan kuma bai rufe wajen da bandeji ba domin hana wasu ƙwayoyin cuta shiga ciki.

Ga bidiyon nan ƙasa:







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button