Labarai

Dole mu tabbatar cewa muna noma abin da za mu ci har mu fitar waje – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya umarci shugabannin ƙasashen Afirka da su mayar da hankali wajen ƙara bunƙasa harkokin noma a nahiyar.

Bbchausa na ruwaito a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ya fitar ya ce shugaba Buhari na jawabin ne a taron harkokin noma da shugabannin kasashen Afirka ke halarta a birnin Dakar na ƙasar Senegal.

Buhari ya yi kira ga takwarorinsa shugabannin ƙasashen Afirka da su rungumi sabbin tsare-tsaren noma domin tabbatar da samar da abincin da zai ciyar da nahiyar har a fitar da shi zuwa ƙasahen ƙetare.

Dole mu tabbatar cewa muna noma abin da za mu ci har mu fitar waje - Buhari
Dole mu tabbatar cewa muna noma abin da za mu ci har mu fitar waje – Buhari

A yayin da duniya ke fuskantar hauhawar farashin kayan abinci sanadiyyar yaƙin Ukraine, musamman kan alkama da masara, shugaban na Najeriya ya zayyano wasu matakan da ya kamata shugabannin Afirka su ɗauka domin sauya wannan matsala.

‘‘Ciyar da Afirka wajibi ne. ‘‘Dole mu tabbatar da cewa muna ciyar da kanmu a yau da gobe da ma kuma nan gaba. Abin da za mu fara yi shi ne mu haɓaka harkokin noma a ƙasashenmu”, in ji Buhari

”Wannan na buƙatar samar wa manoma abubuwan da suke buƙata kamar ingataccen irin shuka da wadataccen takin zamani da sabbin dabarun noma”.

‘‘Idan muna son yin nasara dole mu tallafa wa manomanmu, babu shakka akwai buƙatar taimaka wa manoma, amma ya kamata mu yi haka cikin gaskiya, mu cire musu ɗabi’ar neman rance, a maimakon haka mu tallafa wa manoma”.

‘‘Ya kamata ƙasashen Afirka su ƙara kauɗi a ɓangaren noma a kasafin kuɗinsu, musamman zuba jari domin samar da abubuwan da ake buƙata kamar haɓaka bincike da samar da abubuwan more rayuwa musamman hanyoyi da noman rani da kuma makamashi”, in ji Buhari.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button