Addini

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma – Prof Muhammad Sani Umar R/lemo

Babban shehin malamin addinin Muslunci prof Muhammad Sani Umar R/lemo yayi nasiha da kira zuwa ga hukuma kan canjin kudi inda ya kowa hujjoji guda biyar wanda yayi bayyani dalla dalla.

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma - Prof Muhammad Sani Umar R/lemo
Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma – Prof Muhammad Sani Umar R/lemo

1. Allah (SWT) yakan zo da abubuwa masu dadi da marasa dadi a rayuwa, don su zamanto jarraba wa ga bayinsa, domin ya bayyana wadanda suka fi kyautata ayyukansu. Wajibi ne ga duk wani Musulmi ya rika halarto da wannan ma’ana a zuciyarsa duk sanda ya ga an shiga wani yanayi bako a rayuwa. Ya yi kuma kokarin cinye wannan jarrabawa.

2. Hukumar samar da takardun kudade karkashin babban bankin Kasa, tare da sahhalewar Shugaban Kasa sun yi tunanin sake fasalin wasu takardun kudaden Nigeria domin wasu maslahohi da suka hango da kuma magance wasu matsaloli. Muna musu kyakkyawan zato cikin wannan kuduri nasu, muna kuma fatan a yi nasara cikin hakan.

3. Amma duk da haka, wajen tabbatar da waccan kyakkyawar manufa, talakawa a Nigeria, sun shiga wani mawuyacin hali kuma mai ban tausayi, musamman a kauyukanmu na Arewa. Don haka muna rokon hukumar da wannan abu ya shafa da su duba halin da Jama’a suke ciki, su amsa kiraye-kirayen al’umma na kara wa’adin da suka saka na dakatar karbar tsofaffin kudi, ko kuma su yi wa tsarin gyaran fuska, don fitar da al’umma daga wannan kangi mawuyaci.

4. Shugabanci na kwarai har koyaushe yana aikata abin da zai saukakewa al’umma rayuwarsu ne ta yau da kullum, da kuma sama musu walawala a harkokinsu, da guje wa jefa su cikin tsanani da wahalhalu.

5. Fatanmu hukuma za ta dubi wannan lamari ta kuma yi abin da ya dace. Allah ya musu kyakkyawan jagoranci, ya ba mu zamanan lafiya da arzuki mai dorewa a Kasarmu. Amin.

Muhammad Sani Umar
Doha- Qatar
January, 28th, 2023.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button