Labarai

Bayan kwashe shekaru 20 suna soyayya, saurayi mai shekaru 99 ya auri budurwarsa mai shekaru 40

Wani tsoho dan kasar Kenya mai shekaru 99, Johana Maritim Butuk, ya auri budurwarsa, Alice Jemeli, mai shekaru 40, bayan sun kwashe shekaru 20 suna soyayya, dimokuraɗiya ta ruwaito.

Masoyan hakikan sun yi aure mai ban sha’awa a Soy, yankin Uasin Gishu ranar Asabar, 14 ga watan Janairun 2023.

Bayan kwashe shekaru 20 suna soyayya, saurayi mai shekaru 99 ya auri budurwarsa mai shekaru 40
Bayan kwashe shekaru 20 suna soyayya, saurayi mai shekaru 99 ya auri budurwarsa mai shekaru 40

Sun fara haduwa ne a 2003, a lokacin shekarun Jemeli 20 kacal shi kuma Butuk yana da shekaru 69. Duk da bambanci shekarunsu, soyayyarsu ta cigaba da bunkasa yayin da suke soyayya.

Ya nemi aurenta Jemeli ne a Disamban 2022, yayin da suka fara hada-hadar tarewa don kasancewa tare har abada.

Kamar yadda The Standard ta bayyana, wannan ne auren Butuk na farko kuma bai taba soyayya d a kowa ba sai Jemeli.

Saidai Jemeli tana da yara uku tare da masoyanta ba baya kuma tana farinciki kan yadda Butuk ya amince da ita a hakan.

An yi shagalin aurensu cike da shauki da kauna a wata cocin katolika ta kusa mai suna St Mark’s Soy, kuma wadanda suka je sun ce biki ya yi kyau.

An samu bayani kan yadda ta kula da shi wanda da farko ba ta ganinsa cikin tsaftar da ta dace.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button