Wani Matashi yayi yunkurin kashe kansa saboda budurwasa
Wani Matashi yayi yunkurin kashe kansa saboda budurwasa
“Saurayi Ya Yi Yunkurin Kashe Kansa Ta Hanyar Shan Guba, Saboda Masoyiyarsa Ta Juya Masa Baya A Jihar Kano


Da yammacin yau Talata ne, wani matashi Tijjani Abubakar ɗan asalin unguwar Gama PRP dake yankin karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano ya yi yunkurin hallaka kan sa biyo bayan cin amanar sa da masoyiyarsa ta yi.


Majiyar rariya, Aminci Radio Kano ta rawaito matashin ɗan kasuwa sayar da wayar hannu ta Farm Centre ya yi wannan yunƙurin ne bayan budurwar da ya shirya angoncewa da ita ta ce a kai kasuwa, domin ta samu wanda ya fishi iya tattali da soyayya, baya ga maƙudan kudade da yake kashe mata.”