Labarai

Da Wa’azin Kabiru Gombe da mai wasa da maciji a kasuwa ɗaya su ke– Anas Abba Dala

Wani fitaccen ɗan siyasa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Anas Abba Dala ya raddi ga kalaman sakataren ƙungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Kabiru Haruna Gombe akan ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Anas Dala wanda ɗan jami’yyar PDP ne ya bayyana cewa duk kalaman da Shehin Malamin ya yi akan mahaifiyar Bola Ahmed Tinubu babu kamshin gaskiya.

Da Wa’azin Kabiru Gombe da tallan maganin gargajiya a kasuwa duk ɗaya su ke – Anas Abba Dala
Da Wa’azin Kabiru Gombe da tallan maganin gargajiya a kasuwa duk ɗaya su ke – Anas Abba Dala

Haka kuma ɗan siyasar ya ƙara da cewa wa’azin Shehin Malamin ba shi da maraba da yadda masu tallan maganin basur ke yekuwar a sayi maganinsu a kasuwanni.

Da wa’azin Kabiru Gombe da masu tallan maganin basur a kasuwa duk tafiyarsu ɗaya”

Hakazalika Anas Dala ɗin ya ce tun da Shehin Malamin ya ke bai taɓa saka wani littafi na addini ya karantar da al’umma ba kamar yadda aka saba gani Malamai su na yi a masallatai da zaurukan ilimi, sai kame – kame wanda hakan ya sa ba shi da maraba da masu wasa da maciji.

Da Kabiru Gombe da mai wasa da maciji a kasuwa ɗaya su ke.”

Ɗan siyasar ya kuma zargi Kabiru Gombe da sauran Malamai akan yin shiru musamman a lokacin da ake ƴan Najeriya ke fuskantar kashe – kashe daga gurin ƴan bindiga da garkuwa da mutane da kuma tsadar kayan masarufi.

Anas Abba Dala dai ya yi waɗannan kalamai a wani bidiyo mai tsawon minti bakwai da ya karade shafukan sadarwa na zamani.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button