Labarai

CBN: Dokar Kudi Cigaba Ne Jamaa – Dr. Aliyu U. Tilde

Jama’a don Allah mu rungumi zamani kan abubuwa na cigaba. Idan ba haka ba wallahi za mu ci gaba da zamewa bayi a kasarmu. Please. Please.

Muna da wata mummunar ta’ada wacce a kullum aka kawo tsari sai mu yi tsalle mu ce ba za mu iya ba. Mu yi ta fatar sharri. Mu sa mutane su yi ta nawa. Har abokan zamanmu su yi su wuce mu. Daga baya kuma mu kama kukan an danne mu.

Misali

Misali, kwanan nan da yawanmu muka yi ta cewa Buhari, da ya kawo wannan canjin kudin, zai sake maimaita talauta mutane da ya yi a 1984. Aka yi ta wadaransa da tsinuwa. Ba a je ko’ina ba, ya tabbata yau ba wanda ya rasa ko sisi. Duk wanda ya kai kudi banki an karba. Yanzu har ba masu kaiwa ma. Da ma kudin guda nawa ne?

CBN: Dokar Kudi Cigaba Ne Jama’a - Dr. Aliyu U. Tilde
CBN: Dokar Kudi Cigaba Ne Jama’a – Dr. Aliyu U. Tilde

A Bude Account Kawai

Tun farkon shirin, mun tsinkayi za a kawo ka’idoji na cire gundarin kudi a bankuna. CBN ta fada. Har na yi azarbabin cewa kila a ce N20,000 za a bari a cire a wuni. Ga shi ya tabbata. A sati N100,000. Amma a tiransifa ko miliyan nawa ne kana iya tura wa abokin huldarka a minti daya ba ma a wuni ba. Illa dai kudin ba a hannunka suke ba. Suna cikin banki ne an ajiye maka. Ba a kwace maka ba. Ba a hana maka amfani da su ba. Sigar amfanin ne kawai aka canza.

Abinda kawai ake bukata shi ne kowa ya bude account. Ba wanda kuma aka hana. Kowane irin mutum ne shi akwai irin account din da zai bude. Ban ji yan kudu suna irin kokawan da muke yi ba. Kuma sun fi mu hulda da kudi. Mun fi su yawan jama’a amma sun fi mu yawan accounts a bankuna. Don haka dole su fi mu moriyar kudaden gomnati musamman basukan banki.

Magabata

Allah ya jikan su Sardauna wadanda a lokaci daya da suka hango za a ba da mulkin kai suka tashi tsaye cikin yan shekaru kadan suka karade Arewa da makarantu, suka koya wa mutane duk abinda yan kudu suka iya nan da nan, aka ba da mulki, suka tabbata mun yi rinjaye kuma mafarkin kudu na mallakarmu bai yiyu ba. Dalilin da ya sa suka yi shahada ke nan. Idan na tuna su, na tuna kashe jikin da yanbokonmu suke haddasawa da rashin tabuka komi banda sata da cin amana, banda kalilan a cikinsu, sai in ji hawaye sun zubo mun.

Allah ya jikan su Sardauna. Wallahi da suna da rai da Sardauna da mutanensa sun sa kowa ya bude account nan da nan ta hanyoyi dabam dabam don mu amfana da shirye shiryen Gomnatin Tarayya na tattalin arziki. Bude account din nan wuni daya kawai ake bukata. Amma banda razana mutane ba abinda muke yi. Daga karatun boko har zuwa bude account sai mun yi nawa an bar mu a baya. Ga mu da Sardaunoni har 19, a matsayin Gomnoni, kamar yanda yake Gomna a lokacinsa. Amma ko motsi. Subhanallah.

Da aka ce za a canza tuki ta hannun dama daga hagu a 1972. Nan da nan aka koya wa direbobi har mu yanmakaranta yanda tsarin yake. Da ranar ta zo shi ke nan. Komi ya tafi sambai. Haka canza Fam zuwa Naira da yarda zuwa meters. Nan da nan aka koya wa mutane canjin lissafi watanni kafin mu rubuta National Common Entrance Examination. Haka aka koya mana sabon lisaafin (metric system) da gaggawa, muka je jarrabawa komi ya tafi daidai.

Yanzu

Amma mu yanzu banda razana mutane ba abinda muka iya. Yau, yaranmu a jarrabowin tarayya ko shading a answer sheets ba sa iyawa. Machine kawai sai ya soke takardunsu. Abinda muke koya a firamare shekaru 50 da suka wuce a kasa da sati. Haka muka yi ta korafi a kan CBT exams. A karshe aka fara, ko mun shirya ko bamu shirya ba. Sannan muka bi. Abubuwa da yawa.

Su Sardauna rediyonsu daya tak da talabijin daya. Yau ga mu da kafafe daruruwa amma mun kasa id da sako da zai wayar wa mutane kai. Sai tsabar surutu da korafi (complaint).

Hadari

Tsabar kudi a tsakaninmu ya jawo mana musibu na rashin tsaro kamar fashi da kidnapping, da cin hanci, da magudin zabe, da nawar kasuwanci, dss. Amfani da tiransfa kuwa zai dakile wadannan abubuwa da yawa. Ni na yi a ma’aikatar ilimi na gani. Ya taimaka gaya wajen ba kowane dankwangila da maaikaci da lebura hakkinsa a kammale. Ya sauwake tafiye tafiye da bibiyar hada-hadar kudi da ake yi. Sai mu ce a’a, ba ma son wannan cigaba?

Kasuwanni

Ana batun kasuwanni a daji wai ba network. Ina ake kasuwa inda ba network? Ai kowa fito da kayansa yake daga daji ya kawo kasuwa. Karamar hukumata—Toro—ta fi kowace girma a Nijeriya. Amma ba kasuwar da ba network a cikinta. Kawai mun koma sai mu kintati abu mu fada kuma mu zauna a kai alhali muna kan network muna social media. Wanda ya kawo saniya ko timatir ai dan birni ne. Sai ya yi tiransifa wa bakauyen a kan idanun shugabannin kasuwa in ya kama. Ba wanda zai bi bakauye daji ya kwace kudin. Suna banki. Kuma ka bar ganinsa bakauye, ya san yanda zai wanke ka tas. Ka ba shi amana ka ga. Tuni zai dauke maka network. Kana ce mar bakauye!

Kira da Goyon Baya

Ina kira ga duk ‘yanbokonmu, na turawa da na muhammadiyya, da mu kira mutanenmu zuwa ga cigaba. Abinda duk duniya ta runguma na alheri mu zame a gaba wajen amfani da shi. Mu daina razana al’umma. Please and please. Mu yi biyayya ga hukuma, alabashin idan muka fara aiwatar da shirin, aka samu matsala, sai mu koka a sake duba tsarin a gyara inda ake bukatar gyara.

Ni ina goyon bayan Gomanti ta ci gaba da wannan shiri. Idan da matsala zan zame na farko da zai koka in sha Allahu. Kuma ina yabawa Gomnati da ta cigaba da aiwatar da shirin ba tare da tsoron cewa an kusa zabe ba, zai jawo mata bakin jini. Haka nake son shugabanci. Ko gobe za a jefa kuri’a, idan cigaba ne, a kawo shi.

Shekaru goma zuwa ashirin masu zuwa za su zo da canje-canje masu yawa a fannin kasuwanci, da tattalin arziki, da noma, da ilimi, da tsaro dss. Dole mu zage dantse don tinkararsu ta hanyar da ba za a bar mu a baya ba. Idan ba haka ba, za mu gadar wa na bayanmu bauta.

Allah ya shirye mu.

Dr. Aliyu U. Tilde
Bauchi
8 Disamba 2022

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button