Kannywood

[Bidiyo] Yan Pi Network Tallan Turmi Suka Dauko – Naziru Sarkin waka

Gidan jaridar Dcl Hausa sunyi fira da Shahararren mawakin nan na Arewacin Najeriya Naziru M Ahmad wanda anka fi sani da sarkin waka inda yayi tsokaci game da network din nan da yan Nijeriya suke jiran fashewarsa.

[Bidiyo] Yan Pi Network Tallan Turmi Suka Dauko - Naziru Sarkin waka
[Bidiyo] Yan Pi Network Tallan Turmi Suka Dauko – Naziru Sarkin waka
Sarki waka yace babba matsalar da nan shine rubutun nan na gaba wato “za ta fashe” zata fashe bayan ka mutu.

Mai gabatarwa da shirin yayiwa sarkin waka tambaya akan cewa to anga Lambarka a pi network yah kenan?

Ya amsa masa da cewa eh tabbas number ta ce amma gaskiya ni bana pi sau daya nagansa a wayar wani abokina shine farkon ganinsa da nayi amma ni sam bana pi.

Sarkin waka naziru m Ahamd ya kara da cewa kana tunanin wai kayi zaune kana latsa waya koda ance dare daya Allah kanyi bature amma wai tana fashewa Dangote yaronka ne wanda ya dade yana tara kudi haba dan pi?.

Ga cikakkiyar hirar nan ku saurara da Dcl Hausa nayi da sarkin waka Naziru M Ahmad.

A kwanakin nan naziru yayi wani shagube inda ya wallafa a kafar sada zumunta yana cewa:

“TAMBAYA

Ya hallata a raba Pi a Gado”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button