Uba ya cinnawa ƴaƴan Matar sa 5 wuta saboda ta ƙi yarda su yi kwanciyar aure
Wani magidanci ya cinnawa ƴaƴan matar sa guda biyar wuta bayan ta hana shi su yi kwanciyar aure.


Magidancin mai suna Ojo Joseph mai shekara 54 a duniya ya aikata wannan aika-aikar ne a jihar Ondo. Lamarin ya auku ne a unguwar Fagun cikin garin Ondo a ranar Lahadi 6 ga watan Oktoɓan 2022 da safe. Majiyar mu ta shafin Labarunhausa ta rahoto.
Yadda magidancin ya aikata wannan ɗanyen aikin, Joseph ya fusata ne inda ya cinnawa yaran wuta bayan mahaifiyar su ta ƙi yarda su yi kwanciyar aure. Wanda ake zargin ya watsa man fetur a ɗakin da yaran ke yin barci sannan ya cinna masa wuta.
Ɗaya daga cikin yaran ya ƙone har lahira yayin da sauran suka samu munanan raunika inda ake duba lafiyar su a babban asibitin tarayya dake Owo. Matar sa da tagwayen da suka haifa tare masu watanni sha takwas a duniya sun tsira daga wutar da ƴan ƙananan raunika.
Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin
Da take tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Funmi Odunlami, ta bayyana cewa tuni aka kama magidancin.
Ta kuma ƙara da cewa an fara gudanar da bincike sannan za a kammala kafin a tura wanda ake zargin zuwa kotu bisa zargin sa wuta da kisan kai.
Abuja – Wata mazauniyar burnin tarayya Abuje dake faɗi tashin zama uwa tana neman kyakkyawan mutumin da zai iya sanya wa ta ɗauki ciki.
Wani Labari Wata Hamshakiyar Mai Kudi a Abuja Na Neman Wanda Zai Dirka Mata Ciki, Zata Biya N3m
Tauraruwar mai amfani da kafar sada zumunta, Uwaoma Susan Joseph, ita ce ta bayyana bukatar matar a dandalin Facebookbukatar matar a dandalin Facebook tare da sakaya bayanan matar legit na ruwaito
Yayin da matar mai kuɗi ta shirya biyan duƙ wanda ya ci sa’ar gama wannan aikin Naira Miliyan N3m, ta kuma kafa wasu sharuɗɗa yayin gudanar da lamarin.
Babban dalilin da yasa za’a ɗaure wa mutumin ido shi ne don kar nan gaba ya dawo yana nemanta da ɗansa. Susan tace:
“Suzy dan Allah ki rubutu game da ni, ina bukatar mutumin da zai mun ciki, kyakkyawan mutum. Za’a ɗaure masa fuska duk lokacin da zai kwanta dani kuma zan biya shi.”
“Abinda yasa za’a rufe masa fuska shi ne don kar ya dawo nan gaba yana nemana da ɗan, zan rikenshi har sai an tabbatar na samu ciki sannam zai tafi. Ina zaune a Abuja ni zan kula da komai na kuɗi.”
“Dan Allah ki ɓoye sunana, tace kuɗin da zata biya miliyan uku cas”