Labarai

Matar Da Ta Auri Ƴar Tsana Ta Koka Saboda Yadda Ƴar Tsanar Yaci Amanar ta

A yau din nan majiyarmu ta samu wani labari mai ban al’ajabi wanda duk wanda yaji wannna labari dole abin ya bashi mamaki irin yadda wannan mace duk mazan da a cikin duniyar nan taba samu wanda take so ba sai mutum mutum na roba inda Aliyu Adam Tsiga ya wallafa wannan labarin a shafin na sada zumunta facebook.

Matar Da Ta Auri Ƴar Tsana Ta Koka Saboda Yadda Ƴar Tsanar Yaci Amanar ta
Matar Da Ta Auri Ƴar Tsana Ta Koka Saboda Yadda Ƴar Tsanar Yaci Amanar ta

Matar da ta auri ƴar tsana ta yi ikirarin cewa dangantakarsu tana gab da yankewa bayan saboda yadda ƴar Tsanar ya yaudare ta, ta hanyar aika wa wata mata saƙo ta wayar salula.

Meirivone Rocha Moraes, ƴar ƙasar Brazil, wacce ta auri yar tsana ta bayyana cewa ya yaudareta. Ma’auratan sun yi haɗu da juna ne a wani bikin da mutane 250 suka halarta a watan Disambar da ya gabata.

Matar wadda ta auri ƴar tsana ta bayyana cewa ya ‘yaudare ta’ a lokacin da ma’auratan za su yi bikin cikar shekara na auren nasu.

Meirivone Rocha Moraes, mai shekaru 37, ƴar asalin ƙasar Brazil, ta bayyanawa manema labarai a farkon wannan shekarar bayan da ta bayyana cewa ta hadu da ‘son rayuwarta’ ƴar Tsana mai suna Marcelo.

A cikin sabon labari mai ban mamaki, matar ƴar Tsanar ta yi iƙirarin cewa ‘ya tafi otal tare da wata mata daban ba ita’, kuma ta ce ta sami saƙonni da yawa wanda waccan matar da suka je otal tare ta tuttura masa a wayarsa.

Ta bayyana cewa ta samu ‘ciki’ tare da ƴar Tsanar, ita yanzu burin ta ya cika tunda daman bata buƙatar ta haihu ba tare da aure ba, amma yanzu burin ta ya cika tunda ta samu ciki dashi kuma har sun haihu. Na yi mamakin daga saduwa da Ƴar Tsanar na samu ciki’ kuma na haifi Ɗa mai kama da baban shi.

Meirivone ta ce: ‘Na yi baƙin ciki sosai kuma da ƙyar na iya yin barci a ranar domin ina ƙaunar mijina sosai, amma ya ci amanata.

Saboda wata ƙawata ta faɗa mani cewa ta ga Marcelo yana shiga otal tare da wata mata yayin da na ke kwance a asibiti na tsawon dare uku da kwana uku.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button