Labarai

Matar aure ta bai wa mai kayan miya kyautar N1m, ta bayyana alherin da yayi mata

Wata matar aure mai amfani da suna @abdulshally ta bai wa mutane mamaki da irin karamcinta tare da tuna alherinta.

Matar aure ta bai wa mai kayan miya kyautar N1m, ta bayyana alherin da yayi mata
Matar aure ta bai wa mai kayan miya kyautar N1m, ta bayyana alherin da yayi mata

Matar auren ta bayyana yadda ta nemi wani tsoho mai suna Shehule mai kayan miya inda ta gwangwaje shi da kyautar N1 miliyan saboda kyautatawa mahaifiyar ta da yayi a lokacin tana karama legit na ruwaito

Kamar yadda ta labarta, sai da ta kwashe sa’o’i uku tana neman Shehule a Arkilla dake jihar Sokoto. A cewarta, yana da shagon langa-langa kuma a nan yake siyar da kayan miya, kayan dandano da kuma kayan ciye-ciyen yara.

Na je neman wannan mutumin kirkin a yankin tsohon gidanmu, sai da na kwashe sa’o’i uku ina nemansu. Sunan shi Shehule, idan kana zama ko ka taba zama a Arkilla, Sokoto, tabbas zaka san wannan mutumin. Yana da shagon langa-langa inda yake siyar da kayan miya, kayan dandano da kuma kayan kwalam na yara.”

“Mutum ne mai kirki, mahaifiyata tana aikena in karba mata kaya bashi kuma sai ya bani da yawa. A wasu lokuta, idan na siya ganye, zai kara min da tumatur, kayan yaji da albasa kuma duk kyauta. Yana bani biskit da alawa duk lokacin da naje shagon. Wadannan kananan karamcin yasa ni farin ciki a lokacin ina yarinya.

Ta kara da yin bayanin cewa:

Bana manta mutane iri uku a rayuwata. Wadanda suka taimakeni lokacin ina cikin tsanani, wadanda suka bar ni lokacin ina cikin tsanani da wadanda suka saka ni a mawuyacin hali.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button