Labarai

Abunda Ya Kamata Kiyi Idan Tsohon Mijinki Yafi Wanda Kike Aure Yanzu Iya Jima’i

Wani saka ci da akasarin zaurawa suke yi harma da masu neman su da aure shi ne kin tsayawa suyi magana akan yanayin kwanciyar jima’i kamin aure. Hakan kuma ke zamo illa bayan sunyi aure.

Abunda Ya Kamata Kiyi Idan Tsohon Mijinki Yafi Wanda Kike Aure Yanzu Iya Jima'i
Abunda Ya Kamata Kiyi Idan Tsohon Mijinki Yafi Wanda Kike Aure Yanzu Iya Jima’i

Duk wata bazawara tasan irin gejin bakatarta na jima’i, haka shima namijin dayake da aure ko ya taba aure yasan iya kokarinsa. Idan haka ne mai yasa baza su fito su tattauna akan hakan ba domin gudun matsala bayan auren?
Ga wasu matakan da zaki dauka bayan aure kika fahimci wanda kike aure bai kai wanda kika rabuda shi iya rike wuta ba. Abdul U Tonga ya wallafa

1: Mataki na farko shine ki fito filli kuma karara ki fadamasa kefa babu abunda kike ji game da Jima’i dashi.
Wanan shine abunda kuka gujewa tattaunawarsa amma yanzu ya zama dole kuyi magana akai ko kuma ki ci gaba da cutuwa.

2: Mataki na gaba shine ki fito karara ki fadamasa yadda kike so a miki a lokacin Jima’i ko kamin Jima’i.
3: Ki koya masa bayan kin fadamasa. Nuna masa yadda zai miki ko yadda kike so a aikace.

4: Ki bashi lokaci domin ganin ko ya fahimceki. Kada kice nan take zai iya ko kike so ya iya.
Dole ne kiyi hakuri ki bashi lokacin har ya kwarai.

5: Kiyi kokarin cire tunanin wannan tsohon mijin naki a rai idan ba haka ba kuwa mijin ki daban mai gamsar dake kuma daban.

6: Ki kashe auren idan bazaki iya hakura ba shi kuma ya kasa gamsar dake.
Saboda yadda Jima’i yake da mahimmanci a rayuwar aure, gara ki rabu da mijin domin gujewa sharrin zuciya.

Da fatan matan da suke cikin irin wannan matsalar zasu yi amfani da wadannan dabarun ko matakan maimakon yin zina da aure ko yiwa mijin bakaken maganganu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button