Kalaman Soyayya

Yadda Zaka Jawo Hankalin Mace Ta Soka

Ba duk Mata bane kashe hula yake sa suji suna son namiji ba. Ga wasu hanyoyin da zaka Iya shawo hankalin macce cikin sauki.

Kalaman soyayya Masu Ƙara Ɗanko so da kauna Na Turanci da Hausa
Yadda Zaka Jawo Hankalin Mace Ta Soka

1: Ka Tausasa Muryarka: Kada ka tinkari mace da muryarka idan ba tattausa bane.

Yi kokarin yin zakankan murya domin jawo hankalinta. Mata suna son jin namiji da zakin muryar.

2: Ka Kusanceta: Kada ka nisance mace a lokacin da kake neman shawo kanta. Ka kusanceta ka nuna mata yadda ka zaku da son jin ta amince maka. Kada kayi nisa da ita, kada kuma ka manne mata.

3: Ka Je Mata Da Barkwanci: Kada ka tinkari mace da fuskar shawo ko da nisa da gadara.

Ka tinkari mace da barkwancin abunda zai faranta mata rai da sata dariya.
4: Kada Ka Kurawa Haliltunta Ido: Idan ka tinkari mace a lokacin neman shawo kanta, kada ka sake ka kurawa nonuwanta ko kugunta ido.

Mata sukan ji shankar namijin da zai zura masu idanuwa yana kallon halittunsu. Hakan na sa su dauka, Sha’awarsu namiji yake ba sonsu ba.
5: Kayi Kokarin Hada Idanuwa Da Ita: Yin ido hudu da mace a lokaci neman shawo kanta nasa a samu nasara a kanta.
A lokacin da kake mata magana, yi kokarin ka rika hada idanuwanka da nata domin cimma burinka a kanta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button