Kannywood

Rikicin kannywood: Kotu ta bayar da umarnin Hannatu Bashir ta bayyana a gaban ta

Rikicin jaruman Masana’antar kannywood wanda yanzu shine abunda yake ta yawo a shafukan sada zumunta wanda ta hada furodusa da kuma jarumi Hannatu Bashir da Ali Nuhu wanda har ta kai ya makata kotu domin ganin zata ɓata masa suna a yau ne ankayi zaman farko Shari’ar su da Ali nuhu India Dalafm radio na ruwaito yadda abun ya kasance.

Rikicin kannywood: Kotu ta bayar da umarnin Hannatu Bashir ta bayyana a gaban ta

“Kotun majistiri mai lamba 58, karkashin mai shari’a Aminu Gabari, ta bada umarnin dole jarumar Kannywood, Hannatu Bashir ta bayyana a gaban kotun.

Kotun ta fara sauraron karar da jarumi Ali Nuhu ya shigar da Jarumar Hannatu Bashir dangane da zargin cin zarafin sa .

Yayin zaman kotun na ranar Talata, lauyoyin mai kara da na wadda ake kara sun bayyana a gaban Kotun, sun nuna wa kotu cewa, za su je su yi sasanci, sai dai kotun taki amince wa inda ta bada umarnin dole wadda aka yi kara, wato Hannatu Bashir ta bayyana a gaban Kotu.

Kotun ta sanya ranar 25 ga watan Oktoban da muke ciki, domin ci gaba da shari’ar.

Jarumi Ali Nuhu ya yi karar Hannatu Bashir bisa zargin ta ci zarafinsa, amma jarumar ta ce, abin da ke tsakanin su shi ne sakon da ta aika masa kan gaza cika alkawarin zuwa fara daukar film dinta.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button