Kannywood

Rashin kuɗin makaranta ne yasa na fara film – Adam A Zango

Gidan Radio freedom da ke jihar kano sunyi wata zantawa da jarumi adam a zango inda ya bayyana cewa dalilin fara harka fim a rayuwarsa saboda rashin kudi shiyasa ya koma Masana’antar kannywood kamar yadda sunka zata da shi inda yace cewa.

Jarumi Adam Abdullahi Zango yace, rashin kuɗin ci gaba da karatu ne yasa ya shiga harkar film.

Adam Zango ya bayyana hakan a tattaunawarsa da Freedom Radio.
Yace, gazawar rashin kuɗin ci gaba da karatun ne yasa shi fara sana’ar haƙar ma’adanai, sai dai da ya gano bata karɓeshi ba ya koma harkar film.

Zango yace, shi mutum ne mai son neman na kansa, kuma ya shigo masana’antar kannywood a shekara ta 2003.”Rashin kuɗin makaranta ne yasa na fara film”-Adam Zango

Rahama Sadau ta cacaki Hukumar Kannywood kan Dakatar da Safara’u

Fitacciyar jarumar fim Rahama Sadau ta caccaki masana’antar Kannywood da Hukumar Tace fina-finaI kan yanda aka dakatar da Jaruma Safiya Yusuf wacce aka fin sani da Safara’u bayan bayyanar bidiyonta.

An dakatar da Safara’u daga masana’antar fina-finan Hausa a shekarar 2022 bayan bayyanar bidiyonta. Jaridar legit na ruwaito.

Zakakurar jarumar tace kawayenta ne suka fitar da wannan bidiyonta wanda hakan ya durkusar da sana’arta a wannan lokacin.

Safara’u ta fara shuhura ne a fim mai dogon zango wanda gidan talabijin din Arewa 24 suke haskawa mai suna Kwana Casa’in, tace ta yi zaman gida na tsawon watanni uku domin gujewa zagin jama’a.

Jarumar ta kara da cewa sai da ta kusa goge dukkan asusunta na soshiyal midiya saboda zagin da take sha daga jama’a. Sai dai iyayenta da ‘yan uwanta sun bukaci ta rungumi hakan matsayin kaddara.

Rahama Sadau tayi martani

Sai dai a ranar Litinin, Rahama Sadau ta caccaki MOPPAN da suka dakatar da Safara’u, Premium Times ta rahoto.

An dakatar da Rahama Sadau daga Kannywood a karon farko a watan Maris din 2015.

“Ina jin cewa bai dace masu tace fina-finai da su dakatar da jarumar ba saboda bidiyonta ya bayyana. Yadda suka bi don shawo kan lamarin bai dace ba. Mutum ce kuma hakan zai iya saka ta a damuwa.

Idan ka kalla bidiyon tattaunawar ta da BBC zaka gane cewa bata ji dadin faruwar hakan ba kuma ta shiga damuwa.
“An dakatar dani daga Kannywood sau da yawa amma abin bai taba damuna ba. Duk lokacin da suka sanar da dakatarwan na kan kalla in yi murmushi.

“Safara’u na fama da matsalar kwakwalwa. Mutanen dake dakatarwa ko korar jama’a mutane ne da basu da fuskoki. Ban taba sanin wanda ya dakatar da ni ba a lokacin da aka dakatar da ni saboda basu da fuskoki.

“Tambaya ta garesu shine me yasa suke saurin dakatar da jama’a ko korarsu a kan kuskure kadan? Hakan bai dace ba.”
– Rahama Sadau tace.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button