Labarai

A Tarihin Nijeriya Ba A Ta’ba Gwamnatin Da Talaka Ke Shan Wahala Kamar Ta Buhari Ba –  Cewar Shaikh Lawan Abubakar Shu’aib

Fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Kano Shaikh Lawan Abubakar ya caccaki Gwamnatin Buhari yana mai cewa tun da aka kafa Najeriya talaka bai ta’ba shan wahala kamar a yanzu da Buhari ke mulki ba.

A Tarihin Nijeriya Ba A Ta'ba Gwamnatin Da Talaka Ke Shan Wahala Kamar Ta Buhari Ba -  Cewar Shaikh Lawan Abubakar Shu'aib
Shaikh Lawan Abubakar Shu’aib

Malam Lawan ya bukaci shugabanni da su ji tsoron Allah su sani talakawa na cikin mummunan yanayi, kuma shugabanni su sani su ma talakawa mutane ne kamar yadda shugabanni suke mutane, kuma bayin Allah ne kamar yadda kowa yake, ba kuma Allah ba ya son su ba ne da ya bar su ya d’auki mulki ya damka wa shugabanni.

A cewar malamin “Lokacin Jonathan shinkafa ‘yar Thailand farashin buhunta naira dubu takwas da dari biyar ne, amma a yanzu ta kai dubu talatin da biyar.”

“Wannan gwamnatin muna fada muna kara nanatawa tare da dukkan girmamawa gwamnati ce da ta bambanta da sauran gwamnatoci da aka yi a Najeriya, domin duk wani dan siyasa a Najeriya ko dai ya sayi kuri’un talakawa da kudinsa, ko ya yi cuwa-cuwa ko magudi. Amma wannan gwamnatin talaka ne ya ba ta kudi kuma ya zabe ta. Amma ba a ta’ba sanda talaka ke d’and’ana kud’arsa a Najeriya kamar yanzu ba. Yadda za ka gane lissafin shi ne d’auki dukkanin rayuwa a baya zuwa yanzu, nawa ne farashin buhun shinkafa kafin zuwan gwamnatin nan? Nawa ne farashin dala? Nawa farashin manfetur? Daga wanda ya ninka sau hudu sai sau uku.”

Dole mu yi adalci mu fad’i gaskiya. Mu muka hau kan mumbari muka ce wannan gwamnatin muna kyautata mata zato za ta yi adalci. Don haka dole mu fada mata cewar wannan yanayin da ake ciki bai yi kama da adalci ba. Ba wannan ne abun tashin hankalin ba, babban tashin hankali shi ne kullum sai an kashe talakawa an yi garkuwa da su, sai a ce a zo a yi taron gaggawa na masu ruwa da tsaki, bayan kwana biyu da taron sai a koma gidan jiya.” In ji Shaikh Lawan Abubakar

Ko a kwanakin nan naira ta yi mummunar faduwar da ba ta taba yi a tarihi ba, wanda hakan ke kara sabbaba wahala da tsadar rayuwa. An hakkake cewa matakan Buhari ne na hana ‘yan kasuwa canjin dala da rufe boda suka sabbaba wannan mawuyacin yanayi. Tun da jimawa ne dai ake ta kira ga shugaba Buhari da ya cire gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele wanda ke da hannu dumu-dumu wajen lalacewar Naira kiraye-kirayen da shugaban ya yi watsi da shi.

A mulkin Jonathan kudin kasar Nijar ana samun kowacce jaka a naira 270 amma yanzu sai mutum ya bayar da 1100 za a ba shi jaka guda. Farashin dala kuwa ya kai 750 wanda a lokacin Jonathan ba ta wuce 170-195 lamuran da ‘yan kasa ke kokawa da shi kasancewar Najeriya a yanzu na samun dala wadatacciya duba da yadda farashin gas da fetur ya tashi a kasuwannin duniya, kuma da yawan Malaman da za su iya kawo gyara sun yi shiru da bakinsu saboda sun shiga gwamnatin suna amfana sun gwammace jama’a su sha kowacce irin wahala tun da su suna amfana.

Allah ya kawo mana d’auki.

Daga Imam Indabawa Aliyu

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button