Labarai

Nayi Mafarkin Queen Elizabeth Tana shakawata a cikin Jannatus Firdausi – Adamu Adamu II

Adamu Adamu II wanda ya fito Takarar shugaban kasa a Nigeria karkashin jam’iyyar Apc wanda ya nemi taimakon al’umma domin ya saya kudin form, a shafin na twitter ya wallafa wani rubuta mai dauke da ban mamaki sosai a wajen alummarsa.

Yanzun nan nayi mafarki Queen Elizabeth tana shaqatawa a cikin Jannatul Firdaus. Allah Ya tabbatar da hakan. Ameen!Nayi Mafarkin Queen Elizabeth Tana shakawata a cikin Jannatus Firdausi - Adamu Adamu II

Allah shine mai wuta da aljanna, Saboda Haka bana bakin cikin shigan kowa aljanna.”


Wani shahararren marubucin Datti Assalafy yayi masa zafaffan martani akan wannan rubutun nasa inda yake cewa..

“BOKO AQIDAH KENAN

“Hakika ban taba tsammanin Adamu Garba haka akidarsa take ba, wannan itace akidar ‘yan boko aqidah, Inter-faith, Feminist da Atheists

Amma shin Adamu Garba wa yake son ya burge? kowa ya san amsar, amma duk wanda yayi imani da Qur’ani Littafin Allah ya san matsayin son wadanda basu yadda da Kadaituwar Allah ba, musamman aya ta karshe da take cikin Suratul Mujadala

Don Allah duk wani dan boko akida da yake kauna ko so ko jibintar lamarin al-kuff@ru yaje ya samu Malami ya masa cikakken bayani akan wannan aya ta karshen Suratu Mujadilah wanda ta sauka akan wani Sahabin Annabi (SAW) da ya kattala Mahaifinsa a fagen yaki:
لَّا تَجِدُ قَوْمًا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ يُوَادُّونَ مَنْ حَادَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَوْ كَانُوا آبَاءَهُمْ أَوْ أَبْنَاءَهُمْ أَوْ إِخْوَانَهُمْ أَوْ عَشِيرَتَهُمْ أُولَٰئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ الْإِيمَانَ وَأَيَّدَهُم بِرُوحٍ مِّنْهُ وَيُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ أُولَٰئِكَ حِزْبُ اللَّهِ أَلَا إِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْمُفْلِحُونَ

Allah Sarki rayuwa, sai na tuna lokacin zanga-zangar ENDSARS da wakilan IPOB suka taso Adamu Garba a gaba kamar zasu cinyeshi, har sukayi reporting application dinsa dake kan Google Playstore Google suka cire application din

Haka muka taso muka dinga bashi kariya tare da yunkurin daukar masa fansa, a lokacin sai da mutanen IPOB sukayi reporting Facebook account dina Facebook suka dakatar da ni na tsawon wata guda, ban san haka akidarsa take ba da ban bashi kariya ba

Muna rokon Allah Ya shiryar damu hanyar tsira duniya da lahira”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button