Labarai

Ganduje Ya kwace lasisin ginin nan da ya rushe na kasuwar waya ta beirut inda ya bada umarnin a mayar da wurin filin parking din motoci

Ya kuma kafa kwamiti domin binkice da hukunta wadanda sukayi ginin ba bisa ka’ida ba shafin Gandujiyya Online na wallafa a Facebook

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya bada umarnin ne yayin da ya kai ziyarar jaje ga yan kasuwar tare da mataimakin sa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.

Gwamna Ganduje yayi kira ga dukkanin masu gine-gine da su tabbatar sunyi bisa cika dukkan ka’idoji domin kiyaye rayuka da dukiyoyi al’umma.

Gwamnan ya kara da cewa, gwamnatin sa ba zata zuba ido wasu masu son zuciya suna ganganci da dukiya da kuma rayukan al’ummar sa ba.

WANI LABARIN : KADAN DAGA CIKIN DALILAN DA SUKA SA NA DORA LAIFI AKAN GWAMNATIN KANO

1. Hanyoyi masu kwalta aka dinga fasawa da izinin gwamnatin Kano ana gida shaguna masu bene, Abba hikima na wallafa a shinfsa

2. An toshe manyan kofofin shiga kasuwar da dama anyi shaguna da izinin gwamnati. Wanda ta wannan hanyoyi ruwa ke kwarara.

3. Hukumar KNUPDA da kanta ta dinga sayarwa da kananan yan kasuwar teburan karfe masu dauke da hatimin KNUPDA in ban manta ba akan kudi N80,000 duk daya.a wasu layikan ma irin su Bajallabe layi 2 ko 3 aka yi wadannan tebura akan tsakiyar titi.

4. Ni da kaida lokacin muna tattara hujjojin zuwa kotu mun auna titi mai fadin kafa 60 amma ya dawo kafa 8. Ko mota daya baza ta iya wucewa ba. Saboda son rai mutane wadanda gwamnati ta bari.

5. Da izini ko sahhalewar hukumomin tsara birane da kula da tituna ake duk abun da ake yi saboda aikin su ne basu yi. Ba inda mutune suke yin dai dai a kan kansu in ba’a auwatar da doka.

6. Yan kasuwa da dama sun magantu akan wannan amma aka ki yin komai. Hasali ma a karkashin shugabancin Alh Balarabe Tatari har kotu muka shigar da gwamnatin Kano amma daga karshe aka yi makarkashiya aka cire shi daga shugabancin saboda yaki bada kai.

7. Idan da gaske ake yi wadannan gidajen za’a rushe komai girman su saboda a tsare dukiyoyin mutane. Ba kangwaye da sauran kananan shaguna ba.

Sai an samu matsala sai ace Allah ne ya kawo.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button