Kannywood

Finafinan Hausa basa ɓata tarbiyya dama can yaranku basu da tarbiyya -Nafisa Abdullahi

Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar finafinan Kannywood, Nafisa Abdullahi tayi kalamai masu kaushi akan mutanen dake sukar finafinan Hausa shafin Labarunhausa na ruwaito

Nafisa Abdullahi a wani rubutu da tayi a shafin ta na Twitter tace ko kaɗan finafinan Hausa ba sa ɓata tarbiyyar yara sai dai idan dama can asali yaran ba su samu tarbiyya a gida ba.Finafinan Hausa basa ɓata tarbiyya dama can yaranku basu da tarbiyya -Nafisa Abdullahi

Akwai masu ganin cewa finafinan na gurɓata tarbiyya

Mutane da dama dai na ganin cewa finafinan Hausa na wannan zamanin na zama wani abin gurɓata tarbiyyar yara, musamman yadda ake nuna wasu abubuwan da suka ci karo da al’adar Hausawa.

An sha korafi akan yadda masana’antar ta koma nuna wasu abubuwa waɗanda suka ci karo da ɗabi’a da al’adar Hausawa, sai dai jarumar na ganin cewa masana’antar bata ɓata tarbiyya.

Nafisa Abdullahi ta caccaki masu sukar finafinan Hausa

A rubutun da jarumar tayi ta bayyana cewa ba yadda za a yi mutane su bar yaran su na kallon finanfinan ƙasar Amurka (Hollywood), finafinan Indiya (Bollywood) dana kudancin Najeriya (Nollywood), sannan su buɗe baki suce finafinan Hausa ne ke ɓata tarbiyya.

A kalamanta:

Kuna kallon finafinan Hollywood, finafinan Bollywood da finafinan turanci na Najeriya, sannan ku zo ku ce finafinan Hausa ke ɓata tarbiyya… haba? Kuna barin yaran ku su kalla, suna amfani da wayoyi da yanar gizo, amma…. finafinan Hausa ke lalata tarbiyya. Ba su da tarbiyya dama tun farko.

Mutane da dama sun yiwa jarumar martani. Ga kaɗan daga

@non-melanin ta rubuta:

Tabbas finafinan Hausa na ɓata tarbiyya fiye da sauran finafinai, dalili kuwa ke a matsayinki na Bahaushiya kin fito a matsayinki na ƴar Hausawa kai babu kallabi kin sha kaya a matse a matsayinki na ƴar musulmai, dubunnan jama’a na kallo ciki har da ƙananun yara, su kuwa can Yahudawa addinin su ya yarda musu.

@TheSuleimanAnas ya rubuta:

Wa’inchan ai’ba Hausa suke yi ba

@meerah9253 ta rubuta:

Dalla can yi mana shiru

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button