Labarai

Ƴan sanda sun cafke ɗan shekara 84 ya yi wa ƴar shekara 8 fyade

Yan sanda a Ogun sun kama wani dattijo mai shekaru 84, Stephen Jack, da laifin yi wa ƴar shekara takwas fyaɗe.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana haka a Abeokuta s yau Asabar, inda ya ce wanda ake zargin yana zaune ne a unguwar Okun Owa da ke Ijebu-Ode, kuma ya yi ƙaurin suna a neman ƙananan yara.Ƴan sanda sun cafke ɗan shekara 84 ya yi wa ƴar shekara 8 fyade

Ya ƙara da cewa mahaifin wanda aka kashen ne ya kai rahoton kubucewar Jack ga ‘yan sanda da ya lura cewa ‘yarsa na zubar da jini daga yankinta.

Oyeyemi, Sufeto na ƴan sanda, ya bayyana cewa da aka yi masa tambayoyi, wacce a ka yi wa fyaɗen ta shaida wa mahaifinta cewa Jack ya yi lalata da ita.

Ya kara da cewa an kai yarinyar zuwa babban asibitin Ijebu-Ode domin yi mata magani.

Kwamishinan ƴan sanda a jihar, Lanre Bankole, ya kuma bayar da umarnin a kai Jack sashen binciken manyan laifuka domin gudanar da bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya.

Wani Labari: Ƴan bindiga sun kashe mutane 15 a masallaci a Zamfara

 

Akalla mutum 15 ne suka mutu, wasu kuma da dama suka jikkata a wani harin da a ka kai a wani masallaci a jihar Zamfara..

Kamfanin Dillacin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a Ruwan Jema da ke yankin karamar hukumar Bukkuyum a jihar, inda ‘yan bindigar a kan babura suka nufi masallacin a yammacin ranar Juma’a suka fara harbi kan-mai-uwa da wabi.

Harin na zuwa ne makonni uku bayan da aka sace wasu masallata a masallacin Zugu na karamar hukumar.

A watan Yuli ma ‘yan bindigar sun kai hari a yankin tare da sace mutane da dama domin karbar kudin fansa.

Ana tsammanin dai ƴan bindigar na da sansani kusa da kauyen, abin da ya sa suke matsa ma wa yankin da hare-hare kenan.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button