Kannywood

Mu Ba Mala’iku Ba Ne Da Zamu San Duk Wani Motsin Safara’u – Afakallu

Shugaban hukumar tace finafinai ta jihar Kano, Isma’il Na’abba Afakallu ya mayar da martani ga masu cewa bai kamata a kama Safara’u da Maigidanta Mr 442 ba.

“Ba mu ne muka ce a kama ta don ra’ayin kanmu ba face sai don sun taka dokar jihar Kano, shine doka ta bayar da dama a kama su. Kuma idan mun kama su ƴansanda zamu miƙawa su kuma kammala bincike su gurfanar da su a gaban kotu, ta yanke hukunci daidai da laifin da suka aikata”

A yayin da wakilin jaridar SARAUNIYA NEWS ya tambaye shi shin kowacce doka suka taka?

Kundin tsarin mulkin jihar Kano ya tanadar da dokoki ga Hukumar Tace Finafinai da sai ɗan ko mawaƙi ya cika su sannan ya cancanci gudanar da ayyukan sa a jihar. Safara’u da Mr 442 ba su da rajista da wannan hukuma sannan kuma suna gudanar da ayyukan su a wannan jiha wanda ya ci karo da koyarwar addinin Musulunci da kuma cin karo da kyawawan al’adun jihar Kano”.

SARAUNIYA NEWS: Akwai wanda yayi martani cewa suna ɓoye a jihar Kano kawai ba ku so kama su ba ne?

AFAKALLAHU: Mu ba mala’iku ba ne da zamu san duk wani motsi na Safara’u da Mr 442, a jihar Kano da take da sama da mutane miliyan goma ace mun san duk inda suka shiga ai wannan zance bai kama da hankali ba. Kuma da suka tsorata ma suke ɓuya don kada mu kama su ai wata nasara ce a wajen mu. Kuma mu ba ma burinmu dole sai mun kama su ba, ɓarnar da suke yaɗawa ce muke so su daina.

Ya ce an tabbatar masa suna ɓoye a wani hotel to ka ga a matsayin sa na wanda ya ke ta rubuce-rubuce yana kiransu da tsinannu da kuma la’annannu me zai hana ya zo mu haɗa kai da shi ya ba mu bayanan inda suke mu kama su?

Shin da rubutun da ya ke yi yana aibata su a duniya da ya taimaka mana da bayanai mu kama su a gurfanar da su a gaban kotu wanne ya fi sauƙi?

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button