Labarai

Buhari ya sayawa ƙasar Nijar Motocin Naira Biliyan 1.4B Domin magance matsalar tsaro

Gwamnatin tarayya ta sayi motocin da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.4 domin taimakawa Nijar wajen magance matsalar rashin tsaro.

Gidan Talabijin na Channels TV ya ruwaito cewa Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsare ta Kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan ga manema labarai na fadar gwamnati bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya a yau 3 ga watan Agusta. LIB na ruwaito.

A cewar Ahmed, yin katsalandan ga makwabciyar kasar Jamhuriyar Nijar ba sabon abu ba ne, kuma hakkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da siyan.

Buhari ya sayawa ƙasar Nijar Motocin Naira Biliyan 1.4B Domin magance matsalar tsaro
Ta bayyana cewa shugaba Buhari, wanda ba za ta iya taba tambayar abin da ya yi ba, yana da hakkin ya tantance halin da ya ke ciki tare da bayar da umarni daidai.

Ta kara da cewa tallafin na kudi wanda aka fi mayar da shi domin inganta karfin kare yankunansu, bisa bukatar gwamnatin Nijar shi ma yana da amfani ga kasar.

Da sanyin safiyar yau ne wata takarda daga gwamnati ta ba da izinin siyan motocin ta bayyana a yanar gizo.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button