Labarai

Gwamnatin Nijeriya za ta ƙara haraji kan kiran wayar salula

Nan ba da daɗewa ba ƴan Nijeriya za su fara biyan harajin kashi 12.5 a kan kiran wayar salula bayan da gwamnatin tarayya ke shirin aiwatar da ƙarin harajin kaso 5 na yin waya a ƙasar.

Ministar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare ta Ƙasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da harajin kiran wayar salula a Nijeriya a jiya Alhamis a Abuja.Jaridar Daily Nigerian na ruwaitoGwamnatin Nijeriya za ta ƙara haraji kan kiran wayar salula

Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, NCC ce ta shirya taron.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bayar da rahoton cewa, za a ƙara kashi biyar cikin 100 ne a kan harajin kashi 7.5 cikin 100 da tuni aka ƙara a kan duk kiran wayar salula da s ka yi, VAT, a ƙasar nan.

Ahmed, wacce ta samu wakilcin mataimakin babban jami’in ma’aikatar, Frank Oshanipin, ta ce harajin na kashi 5 cikin 100 da ake shirin aiwatar wa yana cikin dokar kudi: 2020 amma ba a aiwatar da shi ba.

Ta ce an samu tsaikon aiwatar da shi ne sakamakon tuntuɓa da gwamnati ta ke yi da masu ruwa da tsaki.

Ta ƙara da cewa za a riƙa biyan harajin ne a kowane wata, ko kafin 21 ga kowane wata.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button