Kannywood

Kawaye sunci amanar Ummi Rahab

A safiyar yau mun wayi gari da wani al’amari daga masana’antar kannywood wanda wasu sunka fitar da bidiyon ummi rahab a cikin wata shiga da bai dace kowa ya ganta ba.

 

Inda tana cikin kayan da idan ba muharaminta ba ko kawayenta ko mijinta ba bata son su ganta balantana matashiyar jaruma da ke tasowa a masana’antar kwatsam sai gashi munyi kicibis da wannan bidiyo.

Ga abinda shahararren marubucin nan a shafin Facebook ke cewa.

“Nima na ga bidiyo na Ummi Rahab a wani yanayin da bai kamata ba, wasu kawayenta sun mata bidiyo kuma suka fitar da bidiyon saboda tsabagen cin amana

Makiya suna neman tarwatsa rayuwar wannan yarinya marainiya, Wallahi da tayi aure da yafi mata alheri akan wannan rayuwar yaudara cikin fim da take yi

Hakika cin amana tayi yawa a wannan rayuwa, abu mai wahala a wannan zamanin namu shine gane hakikanin masoyi na gaskiya

Duk wanda aka cutar dashi a yau ko akaci amanarsa to akwai sa hannun na kusa da shi wato aboki ko kawa, wani lokacin har da dan uwa na jini

Muna rokon Allah Ya nesanta tsakanin mu da masoyan karya, Ya karemu daga sharrin makiya na fili da na boye.

Daga datti assalafy”

Wannan baiwar Allah yanzu haka tana umrah amma wasu sun na neman ɓata mata suna.

Hausaloaded ta tsaya tayi nazari na shin ya dace ta nunawa mabiyanta wannan bidiyo ko yah?.

Sai munji daga gareku.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button