Labarai

Karuwa Ta Kwashewa Wani Magidanci Kayansa Bayan Da Suka Gama Kece-Raini A Hotel

A yammacin jiya ne wani abu ya faru a wata jiha, nan da nan aka tura mana hoton da labarin domin mu wallafa.

Wani magidanci ne da ya yiwa matarsa karyar cewa zaije taran wani abokin harkarsa da zai zo daga turai. Don haka ba lalle bane ya dawo gida yau.

Bayan sunyi sallama da matarsa ashe daman ya shirya da irin karuwan nan ne da ake haduwa dasu a kafafen sadarwa. Inda ya gayyatota domin su kwana domin su sheke ayarsu.

Sai dai bayan da ta gama jigatashi yayi nauyin bacci. Sai kawai ta sulala ta kwashe kayansa na sawa daya sako yazo wadanda akwai kudi kusan naira miliyan 2 da rabi amma a dalar Amurka suke.

Bayan ya farka ne yaga Babu ita, kuma babu kayansa, anan ne ya rude ya fito daga dakin otel din a guje tsirara. Sai da ma’aikatan otel din ne suka bashi tawul ya daura inda yaje bakin titi yana ta dube-dube wai ko zai ganta yake ambatar kudinsa kundinsa.
(Shine a hoton nan)

To Maza magidanta dai sai ayi hattara. Ga laifi na zina. Ka Karya, yaudara da cin amana. Ga kuma asaran kudin da yayi.

Daga Tonga Abdul TongaMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button