Labarai

ABINDA YA FARU A SOKOTO: Akwai abinda ake kira da “defense of provocation” a criminal law – Barr.Aysha Ahmad Muhammad

Wata kwararriyar Barista a Kaduna tayi sharhi kan abinda ya faru a Sokoto kuma ga yadda sharhin nata wanda ta sanya a shafinta na Facebook ke cewa:

Abinda ya faru a Sokoto abune da duk wani musulmi zaiyi Allah wadai dashi. Babu wani musulmi dake aibata addinin Kirista ko kuma Malamansu a iya sanina. Amma a wani bangaren ba haka bane. A koda yaushe burin masuyin addinin daba musulunci ba shine aibata musulunci da Annabi Muhammad SAW wanda ko a ina ansan yadda cin zarafi ko aibata shi yakan tunzura Musulmi a duk inda yake.”

Lauyar ta cigaba da cewa “Akwai abinda ake kira da “defense of provocation” a criminal law wanda muddin ya tabbata to baa kama wanda ake zargi da aikata laifi kamar yadda ya gudana a wannan case din. Saboda daga lokacin da ta aika da audio din Wazup group dinsu da kuma lokacin da aka aikata abinda aka aikata a akanta yana cikin ya nayin da defense of provocation zai yi tasiri akan wadanda ake tuhuma.”

“Zaiyi kyau Gwamnati ta tsawata iya tsawatawa akan aibata Addinin mutane, Manzannin su, Annabawan su da kuma Malamansu don kuwa babu wanda zai iya jure ko hakurin aibantamai abin bautarsa ko ibadarsa.”

Allah karawa Annabinmu daraja S.A.WMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button