Labarai

Zan fitar da ƴan Nijeriya miliyan 40 da ga talauci nan da shekara 2 – Buhari

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara kokarin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 40 daga kangin talauci nan da shekaru biyu masu zuwa ta hanyar shirin farfado tattalin arziki da ga annobar korona, wanda ta yi masa laƙabi da NG-CARES.

Kodinetan shirin na NG-CARES na kasa, Abdulkarim Obaje ya bayyana hakan a wajen rufe taron bita na tsawon mako guda a Ibadan.

Taron horaswar da aka gudanar a Ibadan, ya samu halartar mutane 440 daga jahohi 36 da babban birnin tarayya, FCT.

Daga cikin mahalarta taron akwai: Jami’an sa ido da tantancewa, Shugabanin bayarwa a Jihohi da Sassan Kula da Jiha a fadin kasar nan.

Daily Nigerian hausa ta ruwaito cewa shirin na NG-CARES yana neman rage radadin annobar korona a kan rayuwar talakawa, manoma, gidaje masu rauni, al’ummomi da kuma masu kananan masana’antu.

Obaje ya ce NG-CARES shiri ne da gwamnatin tarayya ta kirkiro da shi, tare da goyon bayan bankin duniya tare da halartar gwamnonin jihohi 36.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa na cewa shirin zai yi tasiri ga halin da ake ciki na talauci a kasar nan, tare da daukar nauyin ‘yan Nijeriya miliyan 40 kai tsaye.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button