Labarai

Idan Na Zama Gwamnan Katsina Cikin Kwana 100 Zan Karya Lagon Ƴan ta’adda – Majigiri

Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP kuma ɗan takarar gwamna a jahar Katsina, Salisu Yusuf Majigiri ya ce idan ya zama gwamnan jahar zai zo da tsare-tsaren da za su magance matsalar tsaro.

Salisu Majigiri ya bayyana haka ne a yayin wata fira da ya yi da wakilin gidan talabijin na Arise a Katsina a warin gangamin nuna aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

A cikin bayaninsa, Majigiri ya ce idan har ya samu mulkin jahar, cikin kwanaki 100 zai mayar da duk ƴan gudun hijira muhallansu, ya kuma sama ma manoma damar ci gaba da aikin guna tare da buɗe duk makarantun da aka rufe saboda ƴan ta’adda.

Ƴan PDP Da APC Na Kuka Game Da Tsarin Sansanci Da Jam’iyyun Ke Yi Wajen Tsayar Da Ƴan Takara – A Taraba

Al’ummar jihar Taraba sun koka dangane da tsarin sasanci wajen fitar da ‘yan takara a karkashin jam’iyyu kamar dai yadda ake gani jihohi da dama, inda su ka ce wani sabon salo ne na cusa wa jama’a ‘yan takarar da ba su cancanta ba.

Kamar yadda suka bayyana a ranar Litinin, mazauna Taraban sun ce hakan wata barazana ce ga samun kyakkyawan shugabanci domin zai kara ta’azzara take-taken cin hanci da rashawa tare da kara jefa al’umma a cikin kangin talauci.

Koken dai ya fito ne daga bakunan ‘ya’yan jam’iyyun PDP da APC a sa’ilin da su ke magana da manema labaru a Jalingo, babban birnin jihar.

Sun yi kira ga masu ruwa da tsaki a ja’iyyu a jihar ta Taraba da kada su amince da wannan tsari domin kuwa ba zai haifar da da mai ido ba.

A sa’ilin da su ke magana da jaridar Tribune, Jonathan Tsokwa, daga Wukari da Grace Tang, daga Sardauna da kuma Kabiru Zubairu, daga Jalingo, sun ce wannan tsari na masu shi ne, ba na talakawa ba kuma idan har aka kuskura aka cusa masu dantakara, sai ya riga rana faduwa a zabukkan 2023.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button