Labarai

Gwamnonin Nijeriya sun bada tallafin N50m ga waɗanda harin jirgin ƙasa ya shafa

Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, NGF, a jiya Juma’a, ta bayar da gudunmuwar Naira miliyan 50 ga gwamnatin jihar Kaduna domin rabawa wadanda harin bam din da jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su.

Wata sanarwa da Kakakin ƙungiyar, Abdulrazak Bello-Barkindo, ya fitar a Abuja a jiya Juma’a, ta ce shugaban kungiyar kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya bayar da wannan gudummawar a lokacin da ya jagoranci tawagar mutane biyu na ƙungiyar zuwa Jihar Kaduna.

Daily Nigerian hausa ta ruwaito fayemi ya ce tawagar ta je jihar ne domin jajanta wa gwamnati da jama’a kan harin jirgin kasa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, yayin da aka kuma yi garkuwa da wasu da yawa

Shugaban NGF, a lokacin da yake jawabi ga Gwamna Nasiru El-Rufai, ya jajantawa jihar Kaduna da al’ummarta.

Ya bayyana harin a matsayin “mai tayar da hankali matuƙa,” saboda yawan wadanda su ka rasa rayukansu da kuma jikkata.

Fayemi ya ce, “Abin takaici, ‘yan ta’addan sun jajirce wajen ganin sun yi garkuwa da wasu da suka tada zaune tsaye a cikin halin rashin tsaro, wanda ya jefa Kaduna cikin rudani.”

Gwamnan na Ekiti ya nuna mamakin cewa ko wasu makiya gwamnatin jihar ne ko kuma gwamnanta ne, ke kokarin kawar da jihar daga turbar ci gaba.

Fayemi ya yi takaicin cewa “a halin yanzu komai dai koma menene ana tunkarar 2023,” yana mai ba da shawarar cewa, ya kamata a kara kaimi wajen tabbatar da tsaron kasar.

Ya ce a shekarun baya, yankin Arewa-maso-Yammacin kasar nan ya kasance yankin natsuwa da fahimtar juna.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button