Labarai

Ta Watsa Wa ’Yarta Fetur Ta Cinna Mata Wuta Kan Waya

Wata mata mai ’ya’ya biyar ta watsa wa ’yar cikinta man fetur sannan ta cinna mata wuta saboda ’yar ta dauki wayar da mahafiyar ta boye a Jihar Ogun. Jaridar Aminiya trust na ruwaito
’Yan sanda daga Babban Ofishin ’Yan Sanda na Mowe a Jihar Ogun sun tsare matar ne bayan wani makwacinta ya kai musu kara cewa matar ta banka wa ’yar cikinta mai shekara 10 da wuta da gangan.
Makwabcin da suke zaune a gida daya ya shaida wa ’yan sanda cewa matar ta yi wa ’yarta danyen aikin ne saboda wayar dan uwan yarinyar da ta dauko ta ba shi bayan bayan mahaifiyar ta kwace wayar daga hannunsa ta boye.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce bayan samun labarin ne DPO na Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Mowe, CSP Folashade Tanaruno, tare da jami’an binciken kwakwaf daga ofishin suka je suka cafke matar.
Ya ce, “Da aka titsiye matar, wadda ta ce sun rabu da mahaifin yaran, ta bayyana wa ’yan sanda cewa ba ta san abin da ya hau kanta ba a lokacin da ta yi wa ’yarta hakan.”
Oyeyemi ya bayyana cewa an garzaya da yarinyar zuwa asibiti mafi kusa inda daga nan aka tura su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Olabisi Onabanjo domin samun kulawar da ta dace.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Lanre Bankole, ya sa a tsare matar a Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin gudanar da zuzzurfan bincike.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button