Labarai

Ramadan: Ɗalibai za su yi azumi a gida bayan da gwamnatin Kano ta rage mako ɗaya a jadawalin karatu na shekara

Gwamnatin Jihar Kano ta baiwa makarantun gwamnati da ma masu zaman kansu Umarnin rufe makarantu saboda gabatowar Azumin watan Ramadan.
Gwamnatin Kano ta yarda da daidaita jadawalin karatu na makarantun firamare da sakandare n gwamnati da masu zaman kansu a jihar.
Daidaita jadawalin ya biyo bayan koke da iyayen yara suka mika ga gwamnati akan suna rokon gwamnati da a bada hutu ga yaran domin su samu damar yin azumi a watan Ramadan, duba da muhimmanci watan.
A cewar gwamnatin a sanarwar da Hukumar Ilimi ta fitar a yau Talata, za a rage mako daya a kan mako 13 da yakamata a yi a zangon karatu na biyu za a kara shi zuwa ga hutun da aka bayar wanda da sati hudu za ayi a hutun yanzu ya koma Sati Biyar.
Saboda wannan daidaitawar duk makarantun gwamnati da ma masu zaman kansu da ke Jihar Kano zasu rufe makarantu da niyyar hutun Sati Biyar daga 1 ga watan Afrilu zuwa 8 ga wata Mayu.
Kwamishinan ilimi Malam Muhammad Sanusi Sa’id ya roki iyaye da su kula da Yaran su yayin hutun da zai gabato musamman lokacin yanayin tsaro da muke ciki.
Ya kara da cewa su tabbatar da Yaran suna bitar karatun su da sauraran shirye shiryen ilimi yayin hutu.
Sources: Daily Nigerian hausaMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button